Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da fiye da Naira biliyan 1.4 domin taimaka wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomi 17 na jihar.
Wannan kudin za a yi amfani da su domin tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, wanda ta haifar da asarar rayuka, rauni da kuma lalacewar gidaje, hanyoyi, da gine-ginen gwamnati.
- Zirga-Zirgar Ababen Hawa Na Gudana Yadda Ya Kamata Yayin Hutun Mako Guda Na Sin
- Sanata Sani Ya Nemi Tinubu Ya Saki Masu Zanga-zanga Da Ke Tsare
Kwamishiniyar Harkokin Jin-Kai, Mairo Amshi, ta bayyana wannan a yayin wani taron manema labarai bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a ranar Litinin.
Ta bayyana cewa, wannan tallafin kudi yana daga cikin shirye-shiryen gwamnatin domin taimakon wadanda lamarin ya shafa.
Ta ce za a fara rabon Naira 50,000 ga mutum 1,500 a kowace karamar hukuma bayan tattaunawa da shugabannin al’umma, ciki har da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, jami’an tsaro, wakilan mata da matasa, da kuma ‘yan jarida.
“Ina tabbatar muku cewa, kwamitin da za a kafa don raba tallafin ba zai nuna bambanci ba, wajen rabon ba,” in ji ta.