Kasancewar yadda ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a daminar bana ga al’ummomi daban-daban a fadin kasar nan, hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas wato (NEDC) ta samar da tallafin kayayyakin abinci da wadanda ba na abinci ba ga al’ummomi daban-daban da ambaliyar ruwa ta shafa a jihohin da suke shiyyar.
Sanin kowane an samu ambaliya mai karfi a fadin kasar nan a bana, lamarin da ya janyo asaran rayuka, dukiyoyi, gonakai, gidaje, gami da tilasta wa dubban mutane kaura daga muhallansu zuwa neman mafaka. Don haka ne wannan tallafin na NEDC ya zo a lokacin da ake tsananin bukatar shi.
- Alkawurana Ga ‘Yan Nijeriya Kan Tsaro, Zaman Kashe Wando Da Tattalin Arziki — Kwankwaso
- Wakilin Jaridar LEADERSHIP Ya Maka Ado Doguwa A Kotu Kan Yi Masa Mahangurba
Babban daraktan gudanarwa na hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC), Mohammed G. Alkali, ya nuna aniyar hukumar na yin hadin guiwar Gwamnatocin jihohin shiyyar domin lalibo bakin da zare da hanyoyin magance ambaliyar ruwa domin kiyaye barnar da hakan ka iya yi a nan gaba.
A jihar Gombe da ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 da lalata muhallai, gonakai, gidaje da sauransu, hadi da tilasta wa mutane da dama kaura daga muhallansu, hukumar ta tallafa ma wadanda lamarin ya shafa da kayan abinci, kayan sawa da sauran kayan bukatu, wanda kai tsaye suka nuna farin cikinsu da hakan.
Da ya ke mika kayayyakin ga gwamnatin jihar Gombe, Mohammed Alkali, ya ce kayan tallafin da ta bai wa jihar Gombe sun kunshi buhunan shinkafa 10,000, galan din Man gyade 3,000, taburmai 5,000, abun rufuwa 5,000, shadda na maza da zani na mata 8,000, kayan yara 3,000 da sauransu.
A cewarsa, a yayin bikin ranar jin kai da duniya da aka gudanar a kwanaki a Maiduguri babban birnin jihar Borno, hukumar ta yi alkawarin taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi shida da suke shiyyar da zimmar rage musu radadin halin da suke ciki.
Mataimakin gwamnan jihar, Manasseh Jatau ya yi alkawarin raba kayan yadda ya dace ga wadanda aka bayar dominsu.
Ya jinjina wa NEDC bisa tallafin da take samar wa jihar tare da rokon hukumar da ta kara ninka tallafinta ga jihar domin mazauna suke mora yadda ya kamata.
Bayan jihar Gombe, jihar Bauchi ma ta amshi tallafin wanda tunin kayan suka shiga hannun gwamnatin jihar Bauchi da nufin rabawa kai tsaye ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bana.
Alhaji Mohammed G. Alkali ya yi bayanin cewa sun zo jihar Bauchi ne domin mika kyautar kayan abinci da wasu kayan bukatun yau da gobe ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa domin rage musu radadin halin da suke ciki a jihar ta Bauchi.
Goni, ya kuma kara da jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa wannan ambaliyar ruwa da ta shafi jihar a bana da ya shafi wasu sassan jihar.
Ya yi bayanin kayan abinci da na sanyawa da suka bai wa jihar sun hada da buhunan shinkafa dubu 10 (10,000), bargunan rufuwa guda 5,000, atamfa na mata guda 5,000, shadda na maza guda 3,000, tabarma guda dubu biyar (5,000), galan din Mangyeda guda 3,000, rigunan yara guda 3,000 da kuma dukka an mika su ga Gwamnatin jihar Bauchi da nufin rabawa ga wadanda lamarin ya shafa.
MD, ya jinjina wa gwamnan Jihar Bauchi bisa kokarinsa na taimakawa ga wadanda ambaliyar ta shafa, ya yi fatan kayan abinci da wadanda ba na abincin da suka kawo jihar za su rage radadin tare da tallafawa ga wadanda ambaliyar ta shafa a jihar.
Alhaji Goni daga bisani ya yi magana kan ayyukan da hukumar ke gudanarwa a jihar Bauchi da suka hada da aikin hanyar Kirfi zuwa Gombe Abba, da ayyuka a sashin Ilimi, lafiya da sauran fannoni gami da saura da dama.
“Sannan, muna da aikin gina gidaje da ake ciki gaba da yi, sannan da aiki a daya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi da na lafiya na jiha ko na tarayya, da kuma ayyukan su na cigaba da gudana.”
Shi kuwa Gwamna Bala Muhammad na Jihar, ya nuna matukar farin cikinsa bisa wannan tallafin da hukumar ta bai wa jihar, yana mai cewa samar da hukumar NEDC na daga cikin muhimman tarihi da nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a zamansa Shugaban kasa.
Ya ce, hukumar na daga cikin rassan da ke gudanar da ayyukansu da ke zuwa ga talakawa da al’umma kai tsaye, kuma sa a jima ana amfanuwa da ayyukan da suke gudanarwa.
Ya kuma yi jinjina kan yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta na farfado da shiyyar Arewa Maso Gabas da hare-haren Boko Haram ya daidaiya a shekarun baya.
Gwamna Bala ya sanar da bakin nasa cewa tabbas ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a jihar musamman a cikin al’ummomi a karamar hukumar Zaki, ya nuna cewa hatta shi kansa da Gwamnatinsa sun yi kokarin samar da tallafin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa, ya nuna cewa lamarin ne ya yi yawa sosai amma sun yi kokari sosai wajen samar da nasu tallafin a matakin jihar.
Kan hakan ne ya nuna cewa kayan tallafin abinci da na wadanda ba abinci ba da suka samu daga hukumar za su taimaka sosai ga wadanda ambaliyar ta shafa.
Kana, ya jinjina da ayyukan da hukumar ke gudanarwa a jihar da cewa tabbas hakan na taimaka wa rayuwar al’ummar jihar.
Daga bisani ne kuma MD, Alkali ya mika kayan tallafin da suka kawo jihar ta hannun mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Sanata Baba Tela da nufin rabawa ga wadanda lamarin ya shafa.
Kazalika, shi kuwa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jinjina ne tare da yaba wa hukumar ta NEDC bisa samar da kayan tallafi ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Buni ya ce, wannan tallafin ba kawai an yi ne a lokacin da ya dace ba, a’a zai ma taimaka sosai wajen rage wa wadanda abun ya shafa radadin halin da suke ciki.
Ya yi tilawar cewa al’ummomi a Gulani, Jakusko, Gujba, Gaidam da wasu kananan hukumomi da dama a jihar ambaliyar ta musu barna tare da lakume rayuka, dukiyoyi, ciki har da gonakai da lalata kabura da sauransu muhallan jama’a.
Daga bisani NEDC ta hannanta buhunan shinkafa 10,000 masu nauyin kg 25, abin rufuwa (Barguna) 5,000, tabarmai na kwanci da na zama guda 5,000 ga gwamnatin jihar.
Sauran kayan da suka bai wa jihar sun hada da galan din mangyade 3,000, turmin zani 5,000, shadda 3,000 da sauransu.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Idi Barge Gubana, ya gode wa hukumar bisa taimaka wa wadanda lamarin ya shafa a jihar Yobe tare da basu tabbacin cewa kayan tallafin zai dauki tsawon lokaci na taimaka wa wadanda aka basu.
Ya ce, tun lokacin da ambaliyar ruwa ta addabi jama’a a yankuna daban-daban, gwamnatin jihar ta tashi tsaye domin taimaka musu da daukan matakan da suka dace kan lamarin.
Tun da farko MD na hukumar bunkasa shiyyar arewa maso gabas, Mohammad Goni Alkali, ya jinjina wa gwamna Mai Mala Buni bisa kokarinsa da damuwarsa kan ambaliyar da ya shafi wasu yankuna.
Ya ce, sun zo jihar Yobe ne domin jajanta wa al’ummar jihar bisa wannan ambaliyar ta bana, tare da mika tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.
MD din ya ce, tallafin na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na taimaka wa al’ummomi da rage musu radadin halin da suke ciki.
Kazalika da take jawabi mambar majalisar wakilai ta tarayya, da ke wakilmar mazabar Damaturu, Gujba, Gulani da Tarmuwa, kuma shugabar kwamitin majalisar kan NEDC, Hon. Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta yi bayanin cewa ta gabatar da kudiri a gabar majalisar don neman hukumar NEMA da sauran hukumomin da abun ya shafa da su samar da tallafi ga al’ummomin Yobe da ambaliyar ruwa ta shafa.
Ta ce, tabbas wadanda ambaliya ta shafa suna gayar bukatar tallafi da taimako, don haka da bukatar a taimaka musu din. Ta yi kira ga hukumar NEDC da ta gyara hanyar Mutai da ke karamar hukumar Gulani domin saukaka wa al’ummomin yankin hada-hadar kasuwanci.
Haka zancen yake a jihar Adamawa al’ummomi sha daya da ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan ta shafa gami da tilasta wa mutane sama da 1000 kaura daga muhallansu a jihar Adamawa sun samu tallafin kayan abinci da wadanda ba na abinci ba daga wajen hukumar NEDC.
A lokacin da yake gabatar da tallafin ga ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Malkohi a karamar hukumar Yola ta kudu, babban hadimin manajan hukumar NEDC, Farfesa Bobboi Umar, ya ce, hukumar ta taimama wa mutane sama da 1000 a sansanin.
Ya ce, hukumar a karkashin jagorancin Mohammed Goni Alkali ta dukufa wajen taimaka wa jama’an da lamarin ya shafa domin rage musu hadin kunci da suka samu kansu a ciki.
Daga bisani kuma hukumar ta kaddamar da rabon kayan tallafin a yankuna sha daya da ambaliyar ta shafa a fadin jihar.
“Mun kaddamar da rabon kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa kudancin Yola da arewacinta.
“Kayan tallafin sun kunshi kayan abinci, mangyade, barguna, kayan sawa, abubuwan wanka da na tsaftace jiki. Dukka wadannan tallafin an yi ne da zimmar rage wa wadanda lamarin ta shafa radadi,” inji shi.
Da yake maida jawabi a madadin gwamnatin jihar, Dakta Mohammad Sulaiman, babban sakataren hukumar samar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA), ya yaba wa hukumar NEDC bisa samar da tallafin ga al’ummomin arewa maso gabas a kan lokaci.
A jihar Borno kuwa, da ya ke mika kayan tallafi ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Dikwa, gwamna Babagana Umara Zulum da ya samu wakilcin mataimakinsa Hon. Umar Usman Kadafur ya ce hukumar NEDC ta bada tallafin kayan ne da nufin azaga wa wadanda ambaliyar ta shafa.
Ya nuna bukatar daukan kwararan matakan da suka dace domin magance ambaliyar ruwa da dakile abubuwan da ke janyo ambaliyar ruwa domin kiyaye rayuka da dukiyar jama’a.
Kadafur ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati a shirye take ta yi duk mai yiyuwa domin karesu ambaliyar ruwa a nan gaba.