Fadar shugaban kasa ta jajantawa wadanda ambaliyar ruwan jihar Bayelsa ta yiwa barna, inda ta ce tunaninta yana tare da wadanda ibtila’in ya shafa.
Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Laraba, ta ce kiraye-kirayen da wasu bangarori ke yi na cewa dole ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar-Farouq tayi murabus ko a sallameta, sam bai dace ba hakan a irin wannan yanayi.
A cewarsa, kusan kowace jiha a Nijeriya ta fuskanci barazanar ambaliyar ruwan bana.
Ya ce gwamnatin tarayya ta damu da abin da ya faru a Bayelsa kamar yadda lamarin ya shafi sauran Jihohin kasar, ya kara da cewa babu wani rai da yafi wani daraja ko kaskanci.
Ya kara da cewa, “Gwamnati za ta fi bayar da karfi a jihar Bayelsa sannan kuma da duk sauran jihohin da abin ya shafa yayin da ake kara samar da kayan aiki ga hukumomin da ke kula da aikin jinkai a jihohin” in ji shi.