An bukaci gwamnatin tarayya da ta Jihar Filato da su agaza wa al’ummar da ke zaune a gabar Rafin-Dilimi a Unguwar Garba Daho a cikin garin Jos wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna a kwanakin da suka gabata.
Wannan kiran na a cikin kasidar da kansila mai wakiltar jamar’ar Unguwar a majalisar karamar hukumar Jos ta Arewa, Honarable Auwalu Baba Ladan, ya rubuta wa majalisar karamar hukumar wanda kuma aka rarraba wa manema labarai a garin Jos babban birnin jihar a makon da ya gabata.
- Manchester United Ta Kafa Mummunan Tarihi A Watannin Oktoba
- An Nemi Fulani Su Manta Da Bambancin Da Ke Tsakaninsu Don Kubuta Daga Matsalar Tsaro
Takardar wanda take dauke da sa hannun kansilan wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar karamar hukumar, ta bayyana damuwarta bisa yawan gidaje da dimbin dukiya da ambaliyan ruwan ta lalata. Ya ce jimillar gidaje 50 ne ambaliyar ruwan ta lalatasu, yayin da miliyoyin naira suka salwanta.
Honarabul Ladan ya kara da cewa kimanin mutane dubu goma ne ambaliyar ruwan ya raba su da muhallinsu. Acewarsa, ambaliyar ya auku ne a sanadiyar yawan ruwan sama da ake yi.
Shi ma da yake tofa abarkacin bakinsa a zantawar da ya yi da wakilimmu, mai rikon kujerar mai Unguwar Garba Daho, Sagiru Umar, ya nuna bakin cikinsa bisa ta’adin da ambaliyar ruwan ta yi.
Ya ce raban da su ga rafin ya yi irin wannan cika ya kai shekaru goma da suka gabata.
Ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu su agaza wa wadanda iftila’in ambaliyar ruwan ya shafa.