A tarihi, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana yin rashin nasara da gagarumin rinjaye a wasannin da take yin rashin nasara a watannin Oktoba wanda hakan ya zamo wani abun mamaki.
A ranar Lahadin da ta gabata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta doke Manchester United da ci 6-3 a wasan hamayya a gasar Premier League karawar mako na takwas kakar wasa ta 2022 zuwa 2023.
- Asirin Barawon Da Ake Zargin Ya Sace Kudin Da Ake Tarawa A Coci Ya Tonu
- Shin Gwamnatin Birtaniya Ta Saurari Kiran Kungiyar OAS Kan Tsibiran Malvinas
‘Yan wasa Phil Poden da Erling Haaland kowanne ya ci kwallaye uku-uku a raga, sai dai Manchester United ta ci kwallo biyu ta hannun Anthony Martial da kuma sabon dan wasa Antony De Santos.
Sannan magoya bayan Manchester United ba za su manta da watan na Oktoba da kuma sakamakon karawar da suka yi a Etihad ba saboda kungiyar ta buga wasanni hudu a baya tana samun nasara kafin wannan wasan na ranar Lahadi.
Amma kuma kafin wannan fafatawar an ci Manchester United kwallaye da yawa a gasar Premier kuma a cikin watan Oktoba kuma tun bayan da aka sauya fasalin gasar Premier United a shekarar 1992 zuwa 1993 an zazzaga kwallaye da yawa a ragar Manchester United a wasanni shida kenan kuma duk a cikin watan Oktoba Mummunan Tarihin Manchester United A Watannin Oktoba Kafin fara wasan a kakar wasa ta 1996 zuwa1997 Manchester United ta doke Newcastle United da ci 4-0 a gasar cin kofin Charity Shield, karawar da ake yi domin bude labulen kakar gasar Premier League.
Wata biyu tsakani shi ne suka sake fuskantar juna karkashin jagorancin Sir AledFerguson, in da Newcastle ta ci United 5-0 a St James Park kuma tun kafin hutun rabin lokaci Darren Peacock da Dabid Ginola suka ci kwallo kowanne.
Daga baya Les Ferdinand ya kara, bayanda suka koma zagaye na biyu, sai dan wasa Alan Shearer ya ci na hudu daga baya Philippe Albert ya kara kwallo ta biyar a raga.
A ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 1999 Manchester United ta ziyarci filin wasa na Stamford Bridge a lokacin da take kan ganiyarta, bayan da ta yi wasa 29 ba a doke taba tun daga Disambar shekarar 1998.
A lokacin tana rike da kofin, sai dai cikin dakika 30 da fara wasa Gus Poyet ya zura kwallo a ragar Manchester United sannan mai tsaron ragar Manchester United Massimo Talbi ya je ya yi karo da mai tsaron baya Denis Irwin, inda Poyet ya samu kwallo cikin ruwan sanyi ya zura a raga ba kowa a ciki.
Har ila yau, minti 15 tsakani Chris Sutton ya kara kwallo ta biyu sannan an kuma bai wa Nicky Butt jan kati, bayan keta da ya yi wa Dennis Wise sannan daga baya Poyet ya ci kwallo tare da Jody Morris, ya yin da Henning Berg na Manchester United ya ci gida aka tashi karawar Chelsea da nasara 5-0.
Sannan a ranar 23 ga watan Oktoban shekara ta 2012 dan wasa Mario Balotelli ne ya fara cin Manchester United a wannan wasan na hamayya, haka kuma aka je hutu, kungiyar da Roberto Mancini ke jan ragama tana da 1-0.
Bayan da aka koma zagaye na biyu kuma Manchester United tana gara kwallo, sai aka bai wa Jonny Ebans jan kati minti biyu da komawa zagaye na biyu, bayan keta da ya yi wa dan wasa Balotelli.
Daga nan aka ga barakar Manchester United, inda Balotelli ya kara, sannan Sergio Aguero ya zura kwallo a raga – wasa ya koma3-0 sai dan wasan Manchester United Darren Fletcher ya zare wa Manchester United kwallo daya.
Saura minti daya lokaci ya cika kafin alkalin wasa ya tashi karawar, sai Manchester City ta kara uku a raga ta hannun Edin Dzeko da ya ci biyu da kuma Dabid Silba kuma shi ne was an da aka doke Manchester United kwallaye da yawa a gida tun bayan 5-0 da Manchester City ta yi mata a 1955.
Kuma karon farko da aka ci Manchester United shida a filin wasa na Old Trafford, tun bayan 6-0 da Huddesfield Town ta yi da wanda ta sha kashi da ci 7-4 a hannun Newcastle United kwana hudu tsakani duk a 1930.
Bugu da kari, a ranar 4 ga watan Oktoban shekara ta 2020 Bruno Fernandes ya fara ci wa Manchester United kwallo a bugun fenareti a minti na biyu da fara wasa, bayan da Dabinson Sanchez ya yi wa Anthony Martial keta.
Daga baya aka bai wa Anthony Martial jan kati a minti na 20, bayan ketar da ya yi w aErik Lamela a lokacin ana cin Manchester United 2-1 sannan Tanguy Ndombele da kuma Son Heung-min ne suka ci wa kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama kwallayen.
Kafin hutu Harry Kane da Son suka kara cin kwallae, inda Tottenham ke da 4-1.
Suna komawa zagaye na biyu Sege Aurierya kara na biyar, sannan Kane ya ci na biyu a wasan kuma na shida a karawar.
Suma Liberpool, a ranar 24 ga watan Oktoban shekara ta 2021 Shekara 10 da kwana daya bayan da Manchester United ta sha kashi a hannun City 6-1 a filin wasa na Old Trafford sai tawagar ‘yan wasan Jurgen Klopp ta ziyarci United a wasan Premier, kuma minti biyar da fara wasa sai Naby Keita ya ci wa Liberpool kwallo.
Dan wasa Diogo Jota ya kara ta biyu a minti na 13 daga nan Mohamed Salah ya zura biyu a raga sai dai magoya bayan United sun yiwa ‘yan wasansu ihu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a gaban ‘yan kallo 73,000 sannan bayan da suka koma zagaye na biyu ne Salah ya ci kwallo ta uku rigis a karawar.