Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da shirin nan na Gwamnatin Tarayya na raba kuɗin tallafi ga mabuƙata mutum 5,428 a Jihar Neja.
Ministar ta ƙaddamar da shirin ne a Gidan Gwamnatin jihar da ke Minna a ranar Talata.
A taron ƙaddamarwar, ta yi amfani da wannan damar ta jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar ta Neja kan ibtila’in ambaliyar ruwa da ya same su a kwanan baya.
Daga nan ta ba da shawara ga waɗanda za su ci moriyar shirin da su yi amfani da kuɗin tallafin ta hanyar da ta dace domin su inganta rayuwar su ta yau da kullum, sa’annan ta ce kuɗin za su taimaka wa waɗanda bala’in ambaliyar ruwan ya shafa wajen samun sauƙi.
Hajiya Sadiya ta ce: “Burin mu a Jihar Neja shi ne mu raba tallafin tsabar kuɗin ga gungu-gungun mabuƙata mutum 5,428 da aka samo daga yankunan ƙananan hukumomi 25 da ke faɗin jihar.
Ta bayyana cewa: “Shugaba Muhammadu Buhari, ta hanyar tsarin da ya fito da shi na taimaka wa kowa da kowa a al’umma, ya ba da umarnin cewa a tabbatar kashi 70 cikin ɗari na masu cin moriyar wannan shirin su kasance mata ne, sannan sauran kashi 30 cikin ɗari kuma su kasance matasa ne.
“Haka kuma ya ba da umarnin cewa a ware aƙalla kashi 15 cikin ɗari na jimillar masu cin moriyar shirin su kasance ‘yan ƙasar nan ne masu buƙatu na musamman, wato irin su naƙasassu da kuma tsofaffi tukuf a jihar.
“Ana matuƙar fatar cewa waɗanda za su fara cin moriyar shirin za su yi amfani da wannan tallafi wajen inganta rayuwar su, su nemi arziki, su samar da guraben aikin yi, su ɗaga matsayin rayuwar su.”
Ministar ta kuma miƙa kayan abinci da waɗanda ba na abinci ba ga waɗanda ambaliyar ruwan nan ta shafa, sannan ta ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da agaza wa mabuƙata kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta.
A taron, har ila yau, ministar ta ƙaddamar da shirin nan na tallafi na Gwamnatin Tarayya mai taken ‘Government Enterprise Empowerment Programme’ (GEEP) inda aka samu mutum 3,166 da za a ba bashi mara ruwa da ya kama tsakanin N50,000 zuwa N300,000 kowane mutum ɗaya.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani-Bello, ya gode wa Gwamnatin Tarayya da ita kan ta ministar saboda waɗannan shirye-shirye na haɓaka tattalin arzikin ƙasa. A cewar sa, sama da mutum miliyan ɗaya ne aka tsamo daga ƙangin fatara a ƙasar nan ta hanyar su.
Sani-Bello, wanda ya samu wakilci daga Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ahmed Matane, ya yi kira ga ma’aikatar Harkokin Jinƙai, da ta Harkokin Mata da ta Aikin Gona da kuma ta Matasa da Wasanni da su riƙa bin diddigin waɗanda su ka ci moriyar shirye-shiryen haɓaka rayuwa da ke ƙarƙashin su domin su tabbatar da cigaba da kuma nasarorin da ake samu daga wannan lokaci zuwa wannan lokaci.