Ana zargin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da gazawa wajen binciken kudaden da aka wawure a dukkan matakan gwamnati.
Kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam da sanya idanu kan harkar tafiyar da kudaden al’umma (SERAP) wacce ta yi wannan zargin, ta maka shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kotu.
Wadanda aka hada wurin shigar da karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce matakin shigar da karar ya biyo bayan gazawar da gwamnatin tarayya tayi wajen binciken makudan kudaden da aka ce an kashe sama da tiriliyan wajen kula da muhalli a dukkan matakan gwamnati, tun daga tarayya da jihohi da kananan hukumomi daga shekarar 2001 zuwa yau da kuma tabbatar da hukunta wadanda ake zargi da aikata almundahana da dukiyar al’umma.”
A cewarsa, a kwanan baya asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce akalla mutane 600 ne suka mutu yayin da miliyan 1.3 suka rasa matsuguni sakamakon ambaliyar ruwa da ta addabi mafi yawan jihohin kasar, tare da lalata kadarori na biliyoyin kudi.
A cikin kara mai lamba FHC/L/CS/2283/2022 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman kotun da ta “umarci shugaba Buhari da ya gaggauta bincike kan yadda gwamnatoci suka kashe wadannan makudan kudaden kula da muhallin tun daga Matakin tarayya, jiha da kananan hukumomi daga shekarar 2001 zuwa yau.”