Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa ta mamaye a ƙalla unguwanni tara a ƙananan hukumomin Ibaji da Kogi, inda ta lalata gonaki da gidaje tare da raba dubban jama’a da muhallansu. Sakataren hukumar agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Mukhtar Atima, ya bayyana hakan a Lokoja, inda ya ce an buɗe sansanonin rikon ƙwarya 42 domin sauƙaƙa wa waɗanda abin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa a shekarar 2024, ambaliya ta tilasta wa mutane sama da miliyan biyu barin gidajensu a ƙananan hukumomi tara na jihar. Wannan ya jawo lalacewar makarantu, da asibitoci, da hanyoyi, da gadoji, da kuma lalata gonaki, inda manoma musamman masu noman doya suka fi fuskantar asara mai girma. Wasu daga cikinsu sun yi gaggawar girbi kafin lokacin da ya dace don guje wa asarar jarinsu, musamman waɗanda suka karɓi bashi daga bankuna.
- Jihar Kogi Na Cikin Fargaba Yayin Da Kogin Neja Da Benuwe Suka Tumfatsa
- Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
A wasu sassan jihar, ambaliya ta katse manyan hanyoyin shiga da fita, lamarin da ya ƙara tsananta wahalar kai ɗauki. Shugaban ƙungiyar ci gaban Kupa (KUDA), Sa’idu Bn Malik, ya ce ambaliyar ta durƙusar da tattalin arziƙin yankin, ta lalata hanyoyin mota, kuma ta ƙara jefa al’umma cikin barazanar kamuwa da rashin lafiya da jawo rashin tsaro.
A jihar Legas kuwa, ruwan sama mai yawa ya rufe muhimman unguwanni ciki har da Lekki, da Mile 2, da 3rd Mainland Bridge, da Ago Palace. Jama’a sun koka da toshewar magudanan ruwa da kuma rashin gaggawar gwamnatin jihar wajen bada agaji.
Daily Trust ta rawaito cewa, Mazauna yankunan sun ce harkokin sufuri sun tsaya cak, gidaje da kadarori sun lalace, yayin da aka tilasta wa wasu barin motoci su yi tafiya a ƙafa. Wasu kuma sun bayyana yadda aikin gina hanya a Lekki ya kara tsananta cunkoso da halin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp