Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, Dakta Usman Hayatu-Mazadu, ya ce, fiye da gidaje 200 ne suka lalace a kananan hukumomin Zariya da Sabon-Gari sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar.
Duk da hasashen ambaliyar ruwa da gargadin da aka yi, wasu mazauna yankunan sun ki gujewa yankunan, wanda hakan ya janyo hasarar dimbin dukiyoyi, in ji Dakta Hayatu-Mazadu, yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar.
- Birtaniya Ta Ɗaure ‘Yan Nijeriya A Gidan Yari Bisa Buga Takardun Auren Bogi
- Ambaliya Ta Yi Ajalin Mutane 49 A Arewa Maso Gabas – NEMA
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dauki matakan dakile illolin da ambaliyar ke haifarwa, da suka hada inganta magudanun ruwa da kuma wayar da kai kan illar zama a wuraren da ake hasashen ambaliyar ka iya afkuwa.
Daga nan, sai ya bukaci mazauna yankin musamman manoma da su yi amfani da sauran filayen da gwamnatin jihar ta ba su domin noma tare da kwace wa afkuwar irin hakan a nan gaba.