Akalla mutane 236 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a jihohi 27 na tarayyar Nijeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja a bana, kamar yadda wani sabon rahoto da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta fitar a shekarar 2025.
Rahoton ya nuna cewa, kawo yanzu ’yan Nijeriya 409,714 ne abin ya shafa a fadin kananan hukumomi 117, inda dubbai suka rasa matsugunansu da kuma barna mai yawa ga gidaje da gonaki.
- Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
- Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako
Jihar Neja ce ta fi kowacce yawan mace-mace inda mutane 163 suka mutu, sai Adamawa da mutane 59. Taraba na da mutane biyar; Sokoto, uku; Jigawa da Yobe, biyu kowanne; yayin da Gombe da Borno aka samu mutuwar mutum daya kowanne.
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.