• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8 A Lardin Sichuan Na Sin

by Sulaiman and CGTN Hausa
10 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8 A Lardin Sichuan Na Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

A yau Lahadi da karfe 1 na safe agogon kasar Sin, gwamnatin gundumar Hanyuan ta lardin Sichuan na kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru, inda ta ba da rahoto kan halin da ake ciki a fannin aikin ceto bayan abkuwar bala’in ambaliyar ruwa a wani kauyen gundumar jiya Asabar. An ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa sama da mutane 30 ne suka bace sakamakon bala’in. Sa’an nan ya zuwa karfe 10 na daren jiya, an gano gawarwakin mutane 8. Baya ga haka an kwashe mutane 412 zuwa wuri mai tsaro, da samar da jinya ga wasu 12 da suka samu raunuka.

An ce da misalin karfe 2 da minti 30 na safiyar jiya Asabar, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa a kauyen Xinhua, na gundumar Hanyuan, lamarin da ya lalata hanyoyin sadarwa, da hanyoyin mota, da gadojin wurin. Daga bisani nan take karamar hukumar wurin ta kaddamar da ayyukan ceto, inda ta tura tawagogi 23 masu kunshe da ma’aikatan ceto sama da 1,000, zuwa wurin da bala’in ya abku, gami da jibge kayayyakin aiki sama da 1,500, kamarsu jiragen sama marasa matuka, da injunan hakar kasa, da gadoji na gaggawa, da motocin sadarwa a can, inda ake gudanar da ayyukan neman mutanen da suka bace, da sake tsugunar da jama’ar da bala’in ya ritsa da su, da dai sauransu.

A sa’i daya kuma, gwamnatin birnin Ya’an na lardin Sichuan cikin gaggawa ta ware tantuna 500, da barguna 3,500, da gadaje masu lankwasa 3,500, da dimbin fitilu, don a kai su wurin da bala’in ya abku. A halin yanzu, an dawo da hidimar sadarwa, da ayyukan hanyoyin sufuri a wurin, kuma a hankali ana maido da wutar lantarki. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Aboki Mai Natsuwa Shi Ne Wanda Ake Iya Dogaro A Kansa

Next Post

Shugaban Amurka Joe Biden Ya Janye Takarar ZaÉ“en Wa’adi Na Biyu

Related

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

9 minutes ago
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata
Daga Birnin Sin

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

1 hour ago
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

3 hours ago
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
Daga Birnin Sin

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

4 hours ago
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

11 hours ago
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

13 hours ago
Next Post
Shugaban Amurka Joe Biden Ya Janye Takarar ZaÉ“en Wa’adi Na Biyu

Shugaban Amurka Joe Biden Ya Janye Takarar Zaɓen Wa'adi Na Biyu

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
gaza

Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa

May 14, 2025
Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa

May 14, 2025
Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

Tinubu Ya Yaba Wa Sule Lamiɗo A Taron Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwasa

May 14, 2025
Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

May 14, 2025
Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

Yadda Aka Gina Ofishin ‘Yansanda Na Zamani A Abuja

May 14, 2025
JAMB Ta Amince Da Maki 140 Da 100 Mafi Karancin Maki Na Shiga Manyan Makarantu

JAMB: TangarÉ—ar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025

May 14, 2025
A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.