An tabbatar da mutuwar mutum uku sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe awanni ana yinsa a garin Suru na karamar hukumar Dakingari a jihar Kebbi.
Shugaban karamar hukumar, Muhammad Lawal Suru, ne ya tabbatar wa da manema labarai faruwar iftila’in a Birnin Kebbi, babban birinin jihar.
- Fargabar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 13 Ta Karu
- NEMA Ta Raba Kayan Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kwara
Lawal, ya ce, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar rasuwar mutum uku tare da lalata dukiya da ta miliyoyin naira.
Kazalika ya bayyana cewa, baya ga ruwan saman kamar da bakin kwarya, ruwan da ya sauko daga tsaunikan, ya kara haifar da ambaliyar ruwan.
An shafe sama da shekaru 20 yakin na fuskantar kalubalen ambaliya, inda ya kara da cewa, a lokacin shugabancin mulkin tsaffin gwamnonin jihar Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu, sun gina magudanan ruwa don magance kalubalen, amma har yanzu, ba ta sake zani ba.