Mata da dama na sha’awar ganin fatarsu ta yi sumul-sumul musamman ma a ce babu kuraje.
Wannan ganye na dauke da sinadarai da dama wadanda sukan iya dada tsawon gashin mace da sa fuska sheki da gyaran jiki da sauransu.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- Mahara Sun Kashe Kwamandan Jami’an Tsaro, Magoya Bayan APC Sun Jikkata A Ebonyi
Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da za a bi domin amfani da su wajen gyara fata da kuma gashin kai.
Ina so masu karatu su gane cewa, a duk lokacin da na lissafo abubuwan hadin kwalliya guda daya daga cikinsu nake so a yi amfani da shi.
Domin yawan sa wa fuska abubuwa da dama na haifar da fesowar kuraje.
Kodewar fuska: Yawan aiki ko shiga rana na sa fuska ta yi baki ko launinta ya zama biyu.
A samu ganyen ‘aloe bera’ a matse ruwansa sai a matsa ruwan lemon tsami a kwaba a rika shafawa a fuska don daidaita launin wannan fata.
Yaushin fata: Wannan ganye na rage tsufa a fuskar mutum. A matse ruwansa a hada da ruwan ‘rose’ a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti goma zuwa goma sha biyar kafin a wanke a kullum.
Yawan gumi/maiko: A samu ganyen a dan kankare bayansa, sannan a sa ruwa a tukunya a dora wuta sai ya dahu ya yi laushi, sannan a sauke a zuba zuma bayan ya huce, sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 a kullum kafin a shiga wanka.
Gautsin fata: A markada dabino da gurji sai a matsa ruwan ganyen ‘aloe bera’ da ruwan lemon tsami, sannan a shafa a fuska da jiki na tsawon minti 30 kafin a wanke.
Gyaran gashi: A matse ruwan ‘aloe bera’ a hada da man zaitun a kwaba su, su kwabu sosai sannan a rika shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai. Yin haka na sa bakin gashi da kuma dada masa tsawo da karfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp