Gawasa wani nau’i ne na ‘ya’yan itaciya, mai dadin kamshi ga kuma dadi; mafi akasarin mutanen karkara sun fi sanin ta tare da yin amfani da ita, duk da cewa; a halin yanzu ana kawo ta birni kamar yadda ake kawo sauran ‘ya’yan itatuwa.
Haka zalika, wasu da dama sun san amfanin Gawasa ga lafiyar jikin Dan’adam; wasu kuma kwata-kwata ba su sani ba, kawai cin ta suke yi saboda dadi da kuma kamshinta.
Bisa binciken da aka aiwatar na amfanin Gawasa ga lafiyar jikin Dan’adam, an tabo bangarori daban-daban da suka hada da:
Amfani da ita wajen kara karfin mazakuta, ta hanyar amfani da namijin goro da kuma dan cikin Gawasar.
A nan, bayan an cinye Gasawar baki-daya; sai a dauki kwallon nata a fasa shi, har sai an ciro dan da yake cikinsa mai laushin gaske; sannan za a samu yana da gardi irin na Gyaɗa, sai a samu namijin goro a hada da shi a rika tauna su tare; za a yi mamaki kwarai da gaske.
Har ila yau, ana kuma amfani da Gawasa wajen magance cutar hakarkari ta hanyar amfani da man Shanu da kuma kwallon Gawasar.
A nan, bayan an cinye Gawasar ya rage iya kwallon; sai a kona shi ya konu sosai (kwallon). Daga nan, sai a daka shi ya yi lukwi sosai a turmi, sai a samu karamar robar man shafawa a zuba a ciki; a kawo man Shanu a hada da shi a juya ya juyu sosai a rika shafawa a hakarkarin da yeke yin ciwo, da yardar Allah za a rabu da ciwon baki-daya.
Haka nan kuma, ana amfani da Gawasa wajen magance cutar basir. Ga wanda yake fama da cutar basir, sai a nemi Gawasa ko dai a ci ta haka ko kuma a kankari jikinta a busar da shi, a daka a rika shan sa a kunu ko koko.
A bangare guda kuma, za a iya samun sassaken Gawasar a jika a rika sha, shi ma yana da matukar tasiri wajen magance cutar basir da izinin Allah kowane iri ne kuwa