Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi kakkausar suka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa yafe wa wasu mutane da aka same su da laifukan take haƙƙin ɗan adam masu tsanani.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce wannan mataki ya nuna cewa gwamnati ta fifita masu laifi sama da wanda aka zalunta, abin da ke hana adalci ga waɗanda suka sha wahala saboda ayyukansu.
- Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026
- Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
A cewar Amnesty International Nigeria: “Yadda hukumomin Nijeriya suka yi wannan afuwa ya nuna cewa an fi bai wa masu aikata laifuka muhimmanci maimakon tabbatar da adalci da diyya ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu.”
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa wannan mataki zai iya raunana doka, hana gaskiya da ɗaukar mataki, tare da ƙarfafa rashin hukunta masu take haƙƙin ɗan adam a Nijeriya.
Amnesty International ta kuma roƙi Shugaba Tinubu da ya sake duba wannan afuwa, tare da tabbatar da cewa haƙƙin waɗanda abin ya shafa da iyalansu an kare su yadda ya kamata.