Jaridar New York Times ta kasar Amurka ta ruwaito cewa, shugaban Amurka Joe Biden, ya amince da wani shirin sirri da ya shafi nukiliyar kasar a watan Maris, wanda a karon farko ya ambaci shirin dakile kasar Sin bisa ikirarin karuwar makaman nukiliyarta.
A martaninta don gane da batun, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana yayin taron manema labarai na yau cewa, kasar Sin ta damu matuka da rahoton. Ta ce, hujjoji sun tabbatar da cewa, a shekarun baya-bayan nan, Amurka ta yi ta yayata batun barazanar nukiliya daga kasar Sin, wandan ba wani abu ba ne face neman hanyar watsi da hakkin dake wuyanta na kwance damarar makaman nukiliya da fadada makaman da neman fifiko.
- Tinubu Ya Sake Nada Farfesa Sheshe Shugaban Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano
- An Kama Dan Uwan Kwankwaso Da Wasu 4 Kan Badakalar Magani A Kano
Mao Ning ta kara da cewa, makaman nukiliyar kasar Sin ba su kai na Amurka yawa ba. Ta ce kasar Sin na bin manufar kaucewa fara kai hari da makaman nukiliya tare da nacewa ga amfani da makaman domin kare kai kadai. Kuma kasar Sin tana tabbatar da makaman nata na wani mataki mara yawa, kamar yadda ake bukata domin tsaron kasa, kuma ba ta da niyyar takarar makamai da wata kasa.
Ta ce, sabanin hakan, Amurka na nacewa ga amfani da nukiliyar domin hana kai mata hari bisa dogaro da fara kai hari, da ci gaba da zuba jari mai yawa wajen daukaka karfinta na makaman da kuma gyarawa wasu kasashe manufar amfani da nukiliyar don hana kai hari. Ta ce Amurka ita ce babbar mai barazanar nukiliya da kuma kawo hadarin. (Fa’iza Mustapha)