Hukumar karbar koke-koke da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, ta kama wasu mutane biyar da suka hada da Alhaji Mohammed Kabara, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, bisa zargin badakalar samar da magunguna na biliyoyin Naira.
Daga cikin wadanda aka kama akwai Garba Kwankwaso, Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed, wanda dan uwa ne ga Shugaban Jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
- Yadda Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Asibitin Ƙauran Namoda Da Ya Inganta
- Huawei Ya Kaddamar Da Horo Game Da Tsaron Yanar Gizo Ga Jami’an Zimbabwe
Kama shi na da alaka da badakalar da ake zarginsa da shi, wanda ya sanya ayar tambaya kan hannun manyan mutane a cikin lamarin.
Hukumar ta kuma tsare Alhaji Abdullahi Bashir, Shugaban kungiyar Kananan Hukumomin na jihar kuma shugaban karamar hukumar Tarauni.
Ana zargin su ne da hada baki wajen bai wa kamfanin Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 38 da ke fadin jihar, wanda ya saba wa dokokin sayan kayayyakin gwamnati.
Binciken farko ya nuna cewa kananan hukumomin 38 sun biya Novomed Naira miliyan 9.150 domin siyan magunguna.
“Muna da kananan hukumomi 44 a jihar kuma sun yi nasarar karbo Naira miliyan 9.150 daga kananan hukumomi 38 don samar da magungunan da ba a kawo su ba,” kamar yadda wata majiya ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN).
Kabiru Kabiru, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya tabbatar da kamen kuma ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta kudiri aniyar bankado badakalar da ake zargi da kuma tabbatar da cewa wadanda ke da hannu a lamarin sun fuskanci shari’a.
Kabiru, ya kuma tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna tsare a hannun hukumar a lokacin hada wannan rahoto.