• Leadership Hausa
Sunday, August 7, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Daga Birnin Sin

Amurka Da Australia Ne Kadai Suka Nuna Damuwa Game Da Hadin Gwiwa A Tsakanin Sin Da Kasashe Tsibiran Tekun Pasifik

by CMG Hausa
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Amurka Da Australia Ne Kadai Suka Nuna Damuwa Game Da Hadin Gwiwa A Tsakanin Sin Da Kasashe Tsibiran Tekun Pasifik
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ranar 30 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi a rubuce, ga taron ministocin harkokin wajen Sin da tsibiran tekun Pasifik karo na biyu, inda ya yaba da kyakkyawan hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik, wadda ta zama misali a fannonin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da samun moriyar juna da nasara tare.

Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin yana ziyarar aiki a kasashe tsibiran tekun Pasifik.

Ziyararsa ta jawo hankalin kasashen Amurka da Australia da wasu kasashen yammacin duniya, wadanda suka dade suna mayar da kasashe tsibiran tekun Pasifik kamar lambunansu, ko kuma wuraren da ke karkashin shugabancinsu, sun hana wadannan kasashe su zabi kasashen da za su hada kai da su da kansu.

A yayin taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik a wannan karo, kasar Sin ta sanar da ci gaba da kyautata sabbin dandali guda 6, na yin hadin gwiwa ta fuskar rage talauci, da sauyin yanayi, da kandagarkin bala’u, da aikin gona, da cibiyar ciyayin Juncao, wadanda suka biya bukatun kasashe tsibiran tekun Pasifik.

Saboda haka ne ma shugabanni, da ministocin harkokin wajen kasashe tsibiran tekun Pasifik masu halartar taron, suka nuna fatansu na fadada yin hadin gwiwa da kasar Sin, a kokarin ganin jama’arsu sun kara jin dadin zamansu.

Labarai Masu Nasaba

MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

Zurfafa hadin kan kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik, yana taimakawa wajen samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba a yankin Asiya da tekun Pasifik, lamarin da ya nuna cewa, kasashe manya da kanana suna cudanya da juna cikin adalci, suna hada kansu, suna samun nasara tare.

Ya fi kyau kasashen Amurka da Australia su daidaita bukatun kasashe tsibiran tekun Pasifik a tsanake, su dauki hakikanin matakai kamar yadda kasar Sin take yi domin raya wadannan kasashe, a maimakon nuna damuwa kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik kawai. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare
Previous Post

Wata Budurwa ‘Yar Shekara 28 Ta Kayar Da Dan Majalisa A Zaben Fidda Gwani Na APC A Inugu

Next Post

Zaben Atiku: Muna Jan Kunnen Buhari Da APC Kan Matsalolin NDDC – Samarin APC A Neja-Delta

Related

MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
Daga Birnin Sin

MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

3 hours ago
Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

4 hours ago
Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan
Daga Birnin Sin

Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan

5 hours ago
Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana
Daga Birnin Sin

Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana

6 hours ago
Kasar Sin Ta Musanta Zarge-zargen Amurka Game Da Atisayen Da Take Yi A Kewayen Taiwan
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Musanta Zarge-zargen Amurka Game Da Atisayen Da Take Yi A Kewayen Taiwan

1 day ago
Kasar Sin Na Gudanar Da Atisayen Soji A Rawayen Teku Da Tekun Bohai
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Na Gudanar Da Atisayen Soji A Rawayen Teku Da Tekun Bohai

1 day ago
Next Post
Zaben Atiku: Muna Jan Kunnen Buhari Da APC Kan Matsalolin NDDC – Samarin APC A Neja-Delta

Zaben Atiku: Muna Jan Kunnen Buhari Da APC Kan Matsalolin NDDC - Samarin APC A Neja-Delta

LABARAI MASU NASABA

Kidayar ‘Yan Nijeriya Ta 2023: Shugaba Buhari Zai Bude Taron Masu Ruwa Da Tsaki

Kidayar ‘Yan Nijeriya Ta 2023: Shugaba Buhari Zai Bude Taron Masu Ruwa Da Tsaki

August 7, 2022
Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju

Peter Obi Ba Zaiyi Nasarar Lashe Koda Rabin Jihar Nasarawa Ba – Inji Deji Adeyanju

August 7, 2022
Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas

Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas

August 7, 2022
MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

MDD Da Gwamnatocin Kasashe Daban-Daban Sun Sake Jaddada Tsayawa Ga Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

August 7, 2022
Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

August 7, 2022
Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

August 7, 2022
NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi

August 7, 2022
Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan

Sharhi: Yadda Kasar Amurka Ta Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Taiwan

August 7, 2022
Matsalar Tsaro: An Gudanar Da Addi’oi Na Musamman A Yankin Funtuwa

Matsalar Tsaro: An Gudanar Da Addi’oi Na Musamman A Yankin Funtuwa

August 7, 2022
Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana

Cinikayyar Waje Ta Hajojin Sin Ta Bunkasa Da Kaso 10.4 Bisa Dari Cikin Watanni 7 Na Bana

August 7, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.