Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya cewa, yanzu ya tabbata cewa, Amurka ta kasance “daular karya” ta ko wace fuska.
Kakakin ya bayyana haka ne, a matsayin mayar da martani ga rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar a baya-bayan nan, wanda a ciki ta bayyana cewa, wai kasar Sin ta zuba biliyoyin daloli don yada labaran karya a duniya.
- AU Ta Yi Kira Da Kara Zurfafa Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Afirka Da Sin
- Tauraruwar Ronaldo Na Dada Haskawa, Al Nassr Na Ci Gaba Da Jan Zarenta A Saudiyya
Jami’in ya ce, abin da rahoton na ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya kunsa, ko kadan ba gaskiya ba ne, domin ya jirkita shaidu da bayanan gaskiya.
Ya ce, tun daga shirin nan na Operation Mockingbird wanda ya bayar da cin hanci da yin amfani da kafafen watsa labarai don yada farfaganda a zamanin yakin cacar-baka, zuwa batun hodar Iblis da wani hoton bidiyo mai suna “White Helmets” da aka ambata a matsayin shaida na kaddamar da yakin wuce gona da iri a kasashen Iraki da Syria a farkon wannan karni, sannan kuma ga wata babbar karya da aka yi na bata manufar kasar Sin ta Xinjiang, hujjoji da dama sun sha tabbatar da cewa, kasar Amurka “daular karya ce” ta ko wace hanya. Har ma wasu a kasar ta Amurka, irin su Sanata Rand Paul, sun yarda cewa, gwamnatin Amurka ita ce kan gaba wajen yada labaran karya a tarihin duniya.
Kakakin ya kara da cewa, wasu a Amurka na da tunanin cewa, za su iya yin nasara a yakin neman bayanai, muddin suka samar da isasshiyar karya. Amma idon al’ummar duniya a bude yake.
Don haka ya jaddada cewa, ko ta yaya Amurka ta yi kokarin amfani da lakabin “karya” a kan wasu kasashe, jama’a da yawa a duniya sun riga sun ga irin yunkuri marasa kyau da Amurkan ke yi, na ci gaba da neman daukaka matsayinta, ta hanyar sanya karya cikin “sabbin manufofinta na danniya” da neman shafawa wasu bakin fenti. (Ibrahim).