Kwallayen da Anderson Talisca da Crsitiano Ronaldo suka ci ne suka sa Al Nassr ta samu nasara da ci 2-1 ranar Juma’a a gasar cin kofin Saudi Pro League.
Ronaldo wanda aka ajiye a benci a wasan da kungiyar ta lashe kofin Sarki na Ohod ya dawo a matsayin kyaftin din kungiyar Al Nassr a karawar da suka yi da Al Ta’ee kuma ya ci gaba da taka rawar gani.
- Cristiano Ronaldo Ya Zura Kwallaye Uku Rigis A Wasansu Da Al Ahl
- Babu Adawa Tsakanina Da Messi – Cewar Ronaldo
Ronaldo ya ci gaba da zura kwallo a raga kamar yadda ya yi a wasanni biyar da suka gabata. Yanzu yana da kwallaye 10 a wasanni shida da ya bugawa kungiyar Al Nassr a gasar ta Saudiyya.
Al Nassr wadda Luis Castro ke jagoranta na ci gaba da samun nasara a wasanni shida a gasar, tare da samun nasara a gasar cin kofin King da kuma gasar zakarun AFC.
Yanzu tazarar maki daya ne tsakanin masu jan ragamar League din Al Ittihad bayan wasanni takwas.