Sakatatren kasashen wajen Amurka, Antony Blinken, ya tattauana da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya nemi aiki tare da sabuwar gwamnatinsa, ya kuma yi alkawarin karfafa tsarin dimokradiyyyar Nijeriya.
Jami’in watsa labaran gwamnatin Amurka, Mathew Miller, ya bayyana haka a sanarwa da aka raba wa manema labarai.
- Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m A Wajena, Ina Da Hujja –Matawalle
- Sojoji Sun Cafke Masu Kai Wa ‘Yan Bindiga Bayanai 3 Kan Garkuwar Da Aka Yi A Kagarko
“aAyau da safe ne Sakataren harkokuin kasashen waje, Antony J. Blinken ya tattauanna da zababben shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu don jaddada bukatar karin karfafa dangantaka tsakanin gwanatin Amurka da gwamnation Nijeriya mai jiran gado.”
“Sakataren ya lura da cew, yana fatan dangantakar Amurka da Nijeriya zai kara karfi da fatimtar juna tare da karfafa al’ummar kasaehn buyi a cikin gwamnatin zababben shugaban kasa Tinubu, sun kuma tattauna bukatar tafiya da kowa kowa a cikin gwamnati, za kuma ku ci gaba da hadin kai a bangaren tsaro da tattaklin arzki.”
Mai magana da yawun zababben shugaban kasa, Tunde Rahman, yan bayyana cewa, Sakataren harkoki kasashen waje na kasar Amurkan ne ya nemi a yi tattaunawar.
“Tattaunawar da aka yi ta waya ya amfanar kwarai da gaske don an gayawa juna gaskiya a cikin nisahadi an kuma yi tattaunawar ne a ranar Talata,” in ji Rahman.
Ya kuma jaddada aniyarsa na kare aikidar dimjokradiyya, inda ya ce sakamakon zaben da aka yi masa yana nuna cikakken ra’ayin al’ummar Nijeriya ne.
Ya ce, za iyi aiki tukuru don hada kan al’ummar Nijeriya, ta haka za su amfana da tsarin dimokradiyya da ingattaciyar tsarin gudanar da gwamnati.”
Rahman ya ce, Blinken ya sanar da zababben shugaban kasa cewa, in har babu hadin kan kasa, tsaro ci gaba trattalin arziki da sahihin gwamnati, Nijeriya ba za ta tsaya a matsayinta ba a shugabancin kasashen Afrika.