A ranar Litinin 20 ga watan nan, sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan jerin wasu umurni, ciki hadda janye kasarsa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Matakin da ya sa Amurka, wadda ita ce kasar da ta fi yawan fitar da hayaki mai dumama yanayi a tarihi, za ta janye daga yarjejeniyar a karo na 2 a kasa da shekaru 10.
Trump ya dade yana goyon bayan amfani da tsoffin makamashi. A wa’adin shugabancinsa na farko, a karon farko Amurka ta zama kasar da yawan makamashi da ta fitar zuwa ketare ya zarce adadin da ta shigo da shi a cikin shekaru 70 da suka gabata, kana ta zama kasar dake kan matsayin farko wajen samar da man fetur da gas a duniya. Wadannan makamashi sun kuma zama mataki mafi muhimmanci a fannin kiyaye babakerenta a duniya, duba da cewa, tun barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, yawan man fetur da gas da Rasha take fitarwa Turai ya ragu matuka, kana adadin da Amurka take fitarwa zuwa Turai ya yi matukar karuwa.
- An Kashe Na Biyun Turji A Shugabanci Tare Da Fitattun Kwamandojin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Saudiyya Ta Ware Dala Biliyan 100 Don Sabunta Masallatan Harami
Ban da wannan kuma, kasancewar jam’iyyar Republican ta fi samun kuri’u daga jihohin da sana’o’in dake yawan fitar da hayaki mai dumama yanayi. Janyewar Amurka daga yarjejeniyar zai baiwa wadannan sana’o’in saukin cin riba, saboda matakin ya kawar da shingayen rage fitar da hayaki mai dumama iska dake gaban wadannan sana’o’i.
A hannu guda kuwa, Trump ya kawar da manufofi kusan 80 na gwamnatin da ta gabata, wanda hakan ya bayyana rashin dorewar manufofin ‘yan siyasar Amurka, saboda dukkansu na hidimtawa wajen kare moriyarsu kadai, nauyin dake wuyansu a duniya, da muradun jama’a sun zama banza a gare su.
Samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba ya zama dole ga kasashen duniya. Ta hanyar keta hakkin saura don cimma burin kai, Amurka za ta girbi abin da ta shuka. (Mai zane da rubutu: MINA)