Amurka ta sanar da sabbin matakai masu tsauri game da yadda ‘yan Nijeriya za su riƙa samun biza.
Wannan ya shafi musamman waɗanda ke son zuwa ne na ɗan lokaci ba zama na dindindin ba.
- Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
- Firaminsitan Sin: Dole Ne Hadin Gwiwar Brics Ya Gaggauta Kafa Ka’idar Ciniki Da Tattalin Arzikin Duniya Mai Adalci Da Bude Kofa
Wannan sabon tsarin ya fara aiki tun daga ranar 8 ga watan Yuli.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, mafi yawan nau’in bizar da Amurka ke bai wa ‘yan Nijeriya irin ta wucin gadi yanzu za ta kasance ta zuwa sau ɗaya kacal.
A baya, ana ba da biza mai wa’adin shekara ɗaya ko sama da haka, kuma mutum zai iya shiga Amurka sama da sau ɗaya da ita.
Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita.
Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe.
Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp