Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya
An gabatar da wani kudiri da ke neman sanya takunkumin biza da kuma kwace kadarorin ‘yan kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore, a gaban Majalisar Dokokin Amurka.
Dan majalisa Christopher Smith ne ya gabatar da kudirin dokar a ranar Talata. Mambobin kungiyar ne ake zargin suna da “alhakin ko kuma hannu a cikin keta ‘yancin addini” a karkashin Dokar ‘Yancin Addini ta Duniya (IRFA). In ji shi
Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin cin zarafin Kiristoci da sauran tsirarun addinai a Nijeriya.
Dan majalisa Smith ya yaba wa shugaban Amurka Donald Trump kan ayyana Nijeriya a matsayin ‘Kasar da ke da damuwa ta musamman’ (CPC), inda ya ambato cewa, akwai rahotanni da ke cewa, ana kai wa Kiristoci hare-hare a sassan jihohin Benuwe da Filato.














