• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Wadda Ke Tayar Da Yake-Yake A Duniya Ta Haifar Da Rikicin ’Yan Gudun Hijira

by CMG Hausa
2 years ago
Amurka

Yau, ranar ’yan gudun hijira ce ta kasa da kasa. Na zana wani yaro mai suna Alan Kurdi, mai shekaru 3 kacal a duniya, ya mutu kan hanyarsa ta gudun hijira, bayan da ya rasa gidansu sanadiyyar yaki a kasar Sham.

Amma, bakin ciki shi ne, a kullum ana samun yara irinsu Alan Kurdi dake rasa rayukansu saboda yake-yake. Alkaluman kididdiga da hukumar kula da kaurar jama’a ta kasa da kasa ta fitar na nuna cewa, tun daga shekarar 2014, yawan ’yan kasar Sham dake gudun hijira, kuma suka mutu a kan hanyarsu ta neman tsira ya haura dubu 29. Baya ga miliyan 5.4 dake gudun hijira a wasu kasashe, yayin da wasu miliyan 13.5 kuma ke matukar bukatar tallafin jin kai.

  • Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Sakataren Harkokin Wajen Amurka

A halin yanzu, kashi 72% na ’yan gudun hijira a duniya, sun fito ne daga kasashen Sham da Venezuela da Ukraine da Afghanistan da Sudan ta kudu. Rikicin ’yan gudun hijira da wadannan kasashe suke fuskanta na da alaka sosai da Amurka, saboda tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen da kuma amfani da karfin tuwo da gwamnatin Amurka take yi. MDD ta ba da alkaluma cewa, tun barkewar yakin Sham a shekarar 2011, matakan soja da Amurka ta dauka a Sham, sun haifar da mutuwar mutane a kalla dubu 350, yayin da rabin al’ummar kasar ke gudun hijira, ga matsalar gidaje da ta abinci, abin da ya zama rikicin jin kai mafi tsananni tun lokacin da aka kawo karshen yakin duniya na biyu.

An dauki hoton Alan Kurdi wanda ya mutu a gabar teku a shekarar 2015, abin da ya girgiza duk duniya baki daya, tare da sosan ran mutane. Amma ’yan siyasa na Amurka sun nuna halin ko-in-kula, suna ci gaba da daukar matakin soja a duniya. Amurka mai haifar da rikicin ’yan gudun hijira, ba ta kula da hakkin bil Adama, sai moriyar siyasa kawai. Muna fatan a dakatar da yake-yake a duniya, don ceton rayukan kananan yara kamar Alan Kurdi.

Amma wannan fata ba zai taba tabbata a duniya ba, sai ’yan siyasar Amurka sun yi watsi da moriyar kashin kai, sun yi la’akari da hakkin bil Adama, musamman ma hakkin kare rayukan kananan yara a duniya. (Mai zana da rubuta: MINA)

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Gwamnan Bauchi Ya Sake Nada Gidado A Matsayin Mashawarci Kan Yada Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Sake Nada Gidado A Matsayin Mashawarci Kan Yada Labarai

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.