Connect with us

Nahiyar Afirka

Amurka Za Ta Kwashe Sojojinta Da Ke Nahiyar Afirka

Published

on

Jami’an Pentagon sun gayawa jaridar New York Times cewa, tashoshin mayakan Amurka dake kamaru, da Kenya, da Libya da Tunisia duk za a rufe su da zarar sakataren harkokin tsaro Jim Mattis, ya amince da shirin. Amma Amurka za ta ci gaba da barin sojoji masu yawa a Nijeriya da Somalia.
Kamar yadda jaridar ta New York Times ta fada, matakin canji ne da Amurka ta tsara daga yakar ‘yan ta’adda zuwa maida hankali kan manyan yake-yake.
Matakin yana zuwa ne bayan wani harin da mayakan sakai suka kai kan sojojin Amurka a Nijar bara,wadda ya halaka sojojin Amurka hudu, la’marin da ma’aikatar tsaron ta dauki laifin aukuwar sa.
Advertisement

labarai