• English
  • Business News
Sunday, July 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Za Ta Yi Amai Ta Lashe Game Da Dokar Dake Shafar Yankin Xinjiang Da Ta Zartar

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Amurka Za Ta Yi Amai Ta Lashe Game Da Dokar Dake Shafar Yankin Xinjiang Da Ta Zartar
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Amurka ta fara amfani da dokar da ta zartar, na wai “Dokar Hana Aikin Tilas Ga Al’ummar Uygur” a jiya Talata.

Wannan daftarin doka mai cike da karairayi na ikirarin hana shigar da kayayyakin yankin Xinjiang cikin kasar Amurka, sai dai an ba da ainihin shaidun dake tabbatar da cewa, babu aikin tilas a lokacin da ake samar da su.

  • Wang Yi Ya Halarci Taron Bayar Da Rahoton Ci Gaban Duniya

Duk abin da Amurka ta fadi game da aikin tilas a jihar Xinjiang karya ce, mataki ne kawai da ta dauka domin yaki da kasar Sin.

A hakika, ’yan siyasar Amurka sun nuna hali-ko-in-kula game da yanayin samun aikin yi a yankin, kuma yunkurinsu shi ne, shafawa kasar Sin bakin fenti da fakewa da batun hakkin Bil Adam. A sa’i daya kuma, da dakile fifikon da Xinjiang ke da shi wajen samar da kayayyaki, har ma da ware yankin daga tsarin samar da kayayyaki a duniya.

Manazarta na ganin cewa, kaddamar da wannan doka mai cike da yaudara, zai keta zaman oda da dokar cinikayya ta duniya, da kawo cikas ga dorewar samar da isassun kayayyakin da ake bukata a duniya. Ban da wannan kuma, watakila lamarin zai kawo cikas ga wasu kamfanonin Xinjiang dake fitar da kayayyaki zuwa ketare, amma Amurka ba za ta cimma burinta na hana bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba. Kasuwanni mafi girma da Sin take da su da manyan bukatun duniya, za su goyi bayan kamfanonin Xinjiang, haka kuma ba za su rasa karfinsu na takara ba ko kadan, idan Amurka ta rufe kofarta.

Labarai Masu Nasaba

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

A nata bangare, Amurka za ta yi amai ta lashe wajen amfani da wannan doka. Amurkawa masu sayayya ne za su dandana mummmuna tasirin dokar.

A halin yanzu, Amurkawa na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi tsanani da aka gani cikin shekaru 40 da suka gabata. Bisa rahoton da manazarcin kamfanin Moody ya bayar, an ce, yawan kudin da ko wane iyalin Amurka ke kashewa a kowane wata, ya karu da dala 460 idan aka kwatanta da sauran shekarun da suka gabata.

Kamata ya yi, Sin ta dauki mataki mai karfi don kiyaye moriyar da ta dace da kamfanoni da al’ummarta, da kuma kiyaye dorewar tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ita kuma Amurka dake gabatar da karairayi, za ta girbi abin da ta shuka. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnati Ta Bayar Da Umarnin Fara Sabon Gwaji Kan Irin Masara Na ‘Tela Maize’

Next Post

Kasar Sin Ta Shirya Ci Gaba Da Taimakawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya Da Tsaro Da Ci Gaba A Kahon Afrika

Related

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika
Daga Birnin Sin

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

9 hours ago
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 
Daga Birnin Sin

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

10 hours ago
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

11 hours ago
Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya
Daga Birnin Sin

Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

12 hours ago
An Sanya Kaburburan Sarakunan Daular Xixia Ta Kasar Sin Cikin Muhimman Wuraren Tarihi Na UNESCO
Daga Birnin Sin

An Sanya Kaburburan Sarakunan Daular Xixia Ta Kasar Sin Cikin Muhimman Wuraren Tarihi Na UNESCO

14 hours ago
Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa
Daga Birnin Sin

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

1 day ago
Next Post
Kasar Sin Ta Shirya Ci Gaba Da Taimakawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya Da Tsaro Da Ci Gaba A Kahon Afrika

Kasar Sin Ta Shirya Ci Gaba Da Taimakawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya Da Tsaro Da Ci Gaba A Kahon Afrika

LABARAI MASU NASABA

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya

July 12, 2025
Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

Shugaban Guinea Bissau Ya Bayyana Sin A Matsayin Abokiyar Hulda Ta Hakika

July 12, 2025
Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

Akwai Bukatar Manyan Jaruman Da Suka Yi Kudi Su Taimaki Na Baya -Barau Dadin Kowa

July 12, 2025
Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

Wang Yi Ya Yi Karin Haske Game Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Amurka 

July 12, 2025
Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

Yadda Iyaye Ke Rungumar Bokaye Don Samar Wa ‘Ya’yansu Mata Mazaje Masu Kudi

July 12, 2025
Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani

July 12, 2025
Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

Tinubu Ya Baro Brazil Bayan Halartar Taron BRICS Na 2025

July 12, 2025
Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya

July 12, 2025
Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

Tinubu Yana Goyon Bayan Ƙananan Hukumomi Su Ci Gashin Kan Su – Minista

July 12, 2025
Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

Danbun Shinkafa Da Nama Da Kifi

July 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.