Hukumar Bunkasa Tsirrai Ta Kasa ‘National Biotechnology Debelopment Agency (NBDA)’ ta bayana cewa a halin yanzu an fara wani zagaye na gwajin sabon irin masara na ‘TELA Maize’ a wasu jihohin Nijeriya.
Mataimakiyar Shugabar Hukumar, Dakta Rose Gidado, ta bayyana haka a tattaunawarta da manema labarai ranar Laraba a Legas.
- Manoma Sun Koka Kan Hauhawar Farashin Takin Zamani
- Kananan Manoma 31,666 Sun Samu Tallafin Noma Naira Biliyan 5.9 – CBN
Ta ce, manoma za su fara shuka wanan Iri na ‘Tela Maize’ a wannan damunan da muke ciki.
An samar da Tela Maize ne ta hanyar bincike na zamani da ake kira ‘Genetically Modified Organisms (GMO)’ yana kuma da karfin jure wa farmakin kwari da kuma jure wa karancin ruwan sama.
A shekarar 2021 ne gwamnatin tarayyar ta hannun hukumar NBDA ta bayar da izinin cigaba da noma masara a filin Allah saboda ingancinsa kuma baya cutar da muhalli.
Cibiyar Binciken Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar ABU ta samar da irin tare da hadin gwiwar Hukumar Binciken Aikin Gona ta Afrika (AATF), da kuma Hukumar Bunkasa Tsirrar (NBDA).
Dakta Gidado ta kuma lura da cewa a halin yanzu IAR da ke Zariya ce gwamnati tarayya ta ba izinin samar da Irin, ta kuma fara rarraba wa manoma Irin masara a yankunan arewacin kasar nan don nomawa a damunan bana.
Ta ce, za a yi sabon gwajin gwajin masarar ne har sau biyu, za a yi a shekarar 2022 da shekarar 2023 kafin a bayar da izinin samar da shi gadan-gadan don manoma gaba daya a fadin Nijeriya.
Ta kara da cewa, a halin yanzu tuni aka fara amfani da irin masarar Tela Maize a wasu jihohi kamar Adamawa, Kaduna, Kano da Jigawa.
Dakta Gidado ta ce irin Tela Maize yana iya jure farmakin kwari kamar (fall armyworm da stem borers) yana kuma jure rashin issashen ruwa sama.
Ta kuma bayana cewa, Nijeriya na daga cikin kasashe 6 a Afrika da suka rungumi Tela Maize, kasashen sun kuma hada da Kenya, Uganda, Tanzania, Ethiopia, Mozambikue da kuma Afrika ta Kudu.