Kasa da mako biyu gabanin zaben Pakistan da ke tafe, a ranar Talata aka yankewa tsohon Firaminista Imran Khan hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari. Jam’iyyar Khan ‘Tehreek-e-Insaf (PTI)’ na fuskantar kalubale sosai a zaben da ke karatowa.
An yanke hukuncin ne a cikin gidan yarin Adiala, inda ake tsare da Khan tun lokacin da aka kama shi a watan Agustan 2023. Khan na fuskantar shari’o’in kotu da dama, wadanda ya ce, an kirkirar masa su ne domin hana shi tsayawa takara.
- ‘Yansanda Ne Ke Bayar Da Babbar Gudunmuwar Satar Mutane A Nijeriya – Seun Kuti
- Ma’aikatan CBN 1,500 Sun Koma Aiki A Ofishin Legas
Shah Mehmood Qureshi, mataimakin shugaban jam’iyyar PTI, kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar a karkashin Khan, shi ma an yanke masa irin hukuncin da aka yanke wa mai gidansa (Imran Khan).
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, kakakin jam’iyyar PTI ya tabbatar da hukuncin, sannan kuma kafafen yada labaran kasar su ma sun ruwaito hukuncin.
Hukuncin dai da aka yanke musu na da alaka da zargin fallasa wasu bayanan sirri na kasar.
Khan ya jagoranci al’ummar kasar tun daga shekarar 2018 har zuwa hambarar da shi a shekarar 2022 ta hanyar kada kuri’ar rashin amincewa, sakamakon rashin goyon bayan da sojoji suka yi masa.
Khan dai ya kasance mai sukar jami’an soji, inda ya zarge su da yunkurin kashe shi.
Dan rajin kare hakkin dan Adam kuma manazarcin siyasa Tauseef Ahmed Khan ya bayyana hukuncin a matsayin “rashin adalci,” yana mai cewa, wannan ba zai dusashe hasken Khan ba sai dai ma ya kara masa farin jini da soyayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp