Ran 28 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Azali Assoumani murnar ci gaba da zama shugaban kasar Comoros ta wayar tarho.
Xi Jinping ya ce, kasashen biyu aminan juna dake da dankon zumunci. Cikin ‘yan shekarun nan, huldar kasashen biyu ta samu ci gaba cikin sauri, ta kuma samu babban sakamakon hadin gwiwa a fannoni daban-daban, kana kasashen biyu na marawa juna baya kan manyan muradun dake jawo hankalinsu. Sin na dora muhimmanci sosai kan bunkasuwar huldar kasashen biyu, tana mai fatan hadin kai da Comoros don ingiza ci gaban huldar kasashen biyu, ta yadda za a amfanawa jama’ar kasashen biyu. (Amina Xu)
Talla