• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Ƙaddamar Da Cibiyar Ƴan Jarida Ta Afrika Masu Amfani Da Harshen Hausa A Nijar

by Muhammad Bashir
12 months ago
Daga Hagu zuwa Dama 1. Aliyu Rabe Aliyu NTA, Nijeriya 2. Abdullaye Koulibaley: Shugaban Hukumar Radio da Telebijin Na Jamhuriyar Nijar 3. Guimbe Kochi Ragiou; Magatakardan Gwamnan Birnin Niamey 4. Hajiya Mariam Lawali Sarki Azbin; Shugabar Kungiyar Yan'jarida Na Afrika masu amfani da Harshen Hausa 5. Mamman Idi Liman 6. Barau Tandja

A ƙoƙarin da ake na bunƙasa ayyukan yan jarida masu amfani da harshen hausa a Nahiyar Afrika, an ƙaddamar da cibiyar ƙungiyar a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Wannan ne karo na farko da aka samar da irin wannan ƙungiya bisa la’akari da jajircewar da ake yi na ganin an bunƙasa harsunan cikin gida musamman Hausa, wanda yake ƙoƙarin mamaye sauran harsuna a nahiyar Afrika.

  • Nijar Za Ta Fara Tattara Bayanan ‘Yan Ta’adda
  • Mataimakin Shugaban Sin Ya Gana Da Firaministan Jamhuriyar Nijar

A yayin ƙaddamar da cibiyar ƙungiyar tare da kwarkwaryar zantawa da yan jaridu na ƙasa da ƙasa, da sauran wakilai da suka zo daga sassa daban daban ciki har da Nijeriya, masu ruwa da tsaki a wannan taro sun bayyana muhimmancin wannan ƙungiya wadda take da manufar aiwatar da aikin jarida nagartacce musamman zaburar da jama’a akan muhimmancin gina al’umma da samar da ci gaba mai ɗorewa.

Maryam Sarki Azbin wadda ta zama jigo wajen samar da wannan ƙungiya tace lokaci ya yi da za a riƙa amfani da harshen cikin gida wajen isar da muhimman saƙonni ga al’umma a duk inda suke.

Sarki Azbin ta bukaci yan jarida dasu kaucewa abubuwan da suke ɓata wa aikinsu kima a idon jama’a kamar izgilanci, da maula, da kwaɗayi, da banbaɗanci da keta mutuncin masu faɗa a ji.

LABARAI MASU NASABA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

Ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta yan’jarida zata yi dukkan mai yiwa wajen zaburar da yan jaridu akan yadda zasu rika amfani da harshen Hausa wajen sanar da mutane abubuwan da zasu amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum.

A jawabinsa, shugaban hukumar gidan telebijin da radiyo na jamhuriyar Niger, RTN, Abdoulaye Koulibaly ya bayyana cewa aikin jarida aiki ne da yake buƙatar gaskiya da sanin makamar aiki, a don haka kuskure ne yan jarida suke yi wajen bada labarai na shaci-faɗi don son abin hannu wasu masu faɗa a ji, ko kuma nuna bangaranci yayin fitar da labarai.

Daga Hagu zuwa Dama1. Aliyu Rabe Aliyu NTA, Nijeriya 2. Abdullaye Koulibaley: Shugaban Hukumar Radio da Telebijin Na Jamhuriyar Nijar 3. Guimbe Kochi Ragiou; Magatakardan Gwamnan Birnin Niamey 4. Hajiya Mariam Lawali Sarki Azbin; Shugabar Kungiyar Yan'jarida Na Afrika masu amfani da Harshen Hausa 5. Mamman Idi Liman 6. Barau Tandja
Daga Hagu zuwa Dama
1. Aliyu Rabe Aliyu NTA, Nijeriya
2. Abdullaye Koulibaley: Shugaban Hukumar Radio da Telebijin Na Jamhuriyar Nijar
3. Guimbe Kochi Ragiou; Magatakardan Gwamnan Birnin Niamey
4. Hajiya Mariam Lawali Sarki Azbin; Shugabar Kungiyar Yan’jarida Na Afrika masu amfani da Harshen Hausa
5. Mamman Idi Liman
6. Barau Tandja

Koulibali yace samar da wannan ƙungiya wata dama ce da zata taimaka wajen magance ƙalubalen da yan jarida suke fuskanta ta fannin gudanar da ayyukansu musamman wajen amfani da harshe na cikin gida.

Sauran waɗanda suka yi jawabi a wurin sun gamsu da tsare-tsare da manufofin da aka gina ƙungiyar akan su musamman tabbatar da hadin kai da mu’amala a tsakanin yan jarida na ƙasashe 11 dake Nahiyar Afrika suna masu cewa yawan da yan jaridar Hausa da ake da su a Nahiyar, sun isa su taka gagarumar gudunmawa wajen magance ƙalubalen da ake fuskanta, da kuma ƙarfafawa masu madafun iko gwuiwa wajen ganin sun yi abin da ya dace na kyautata rayuwar al’ummar yankin.

Aliyu Rabe Aliyu Ma’aikaci a hukumar Telebijin a tarayyar Nijeriya (NTA), ya ce, babban aikin da ƙungiyar ƴan jarida masu amfani da harshen Hausa za ta sa a gaba shi ne sauya fasalin aikin jaridar gado na ‘yan ku ci ku bamu, ya zuwa aikin jarida na samar da mafita ga tulin ƙalubalen da yankin yake fuskanta ta hanyar amfani da harshen da kowa yake sonsa, kuma yake amfani da shi watau harshen HAUSA.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Labarai

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Labarai

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

October 31, 2025
Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
Labarai

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Next Post
Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci CIIE Karo Na 7

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.