Wutar lantarki ta ɗauke a sassa daban-daban na Nijeriya a ranar Laraba bayan da babbar tashar wutar lantarki ta sake faɗuwa.
Lamarin ya faru tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na rana, inda wutar da ake samu ta ragu.
- Gwamnatin Kaduna Ta Umarci Makarantu Masu Zaman Kansu Da Su Nemi Amincewarta Kafin Ƙara Kuɗi
- Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna
Kamfain rarraba wutar lantarki (DisCos) ya sanar da ɗaukewar wutar.
Kamfanin rarraba wutar Abuja (AEDC) ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga rasa wuta daga babbar tashar lantarki da misalin ƙarfe 11:23 na safe.
Haka kuma, Kamfanin rarraba wutar Fatakwal (PHED) ya tabbatar da cewa babu wuta a jihohinsa guda hudu: Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, da Kuros Riba.
Dukkanin kamfanonin sun roƙi abokan hulɗarsu da su yi haƙuri, inda suka ce injiniyoyi na aiki don gyara wutar.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar lantarkin yanzu haka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp