Gwamnatin Tarayya ta ɗauki hayar zaratan sojoji daga ƙasashen waje domin horas da dakarun ƙasar nan kan dabarun yaƙi da ‘yan ta’adda da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ministan Tsaro, Badaru Abubakar ne, ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da horas da sojojin Nijeriya 800 a Kaduna, inda ya ce za a bai wa sojojin sabbin kayan aiki da dabarun zamani domin tunkarar matsalar tsaro.
- Kiyaye Ci Gaba Mai Dorewa A Huldar Sin Da Amurka Ya Dace Da Moriyar Sasssan Biyu
- Matasa Sun Daka Wawasu Kan Tirelar Kayan Agajin Ramadan Na Seyi Tinubu A Gombe
A cewar ministan, sojojin Nijeriya 2,400 ne za su fara samun wannan horo a zagaye na farko, sannan daga baya wasu ƙarin 800 su biyo baya.
Duk da cewa ba a bayyana ƙasashen da za a ɗauko waɗannan sojojin ba, an bayyana cewa su fito ne daga ƙasashe bakwai.
Dalilin Horas da Sojojin
Nijeriya na fuskantar matsalar tsaro daga ƙungiyoyin ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan ta’adda.
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka.
Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar.
Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp