Wasu gungun ‘yan banga sun bindige wasu ‘yan bindiga uku a wani yunkurin kai hari a ofishin ‘yan sanda da ke jihar Anambra.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa an kashe ‘yan bindigar ne a safiyar ranar Litinin a lokacin da suka yi yunkurin kai hari ofishin ‘yan sanda na Awada da ke kusa da garin Obosi a karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.
Yayin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Ikenga Tochukwu, har yanzun bai ce uffan ba dangane da lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton, sakataren yada labarai na gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, Mista Christian Aburime, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp