Wannan rana ce ta bakin ciki ga al’ummar kauyen Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe yayin da mazauna kauyen suka taru domin jana’izar mutane 77 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe a ranar Lahadi.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, an tsinto gawarwakin mutanen da aka kashe ne a cikin garin bayan harin da ‘yan Boko Haram suka kai wa al’ummar a ranar 1 ga Satumba, 2024.
- Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Zuwa Jana’izar Mahaifiyar Yar’Adua
- Kwamitin Majalisa Ya Nemi A Rage Wa ‘Yan Majlisa Albashi
Da ake zantawa da daya daga cikin Hakiman gundumar, Alhaji Alimi Kupti, ya ce, “Yanzu mun tabbatar da cewa harin da aka kai a garin Mafa a wannan makon shi ne mafi muni da ‘yan Boko Haram suka kai a wannan yankin, inda suka kashe mutane da dama ciki har da yara kanana da tsofaffi.
Ya kara da cewa, “Mun kuma iya tabbatar da kone-konen gine-gine yayin da ‘yan Boko Haram suka kai mummunan harin.”
Tuni dai aka yi jana’izar Mamatan a Babbangida, hedikwatar karamar hukumar mai tazarar kilomita 50 daga Damaturu, babban birnin jihar, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, ‘yan banga da shugabannin al’umma.