A yau Litinin ne, aka bude bikin baje kolin fina-finai kan shawarar “Ziri daya da hanya daya” a hukumance ta kafar bidiyo, wanda babban gidan rediyo da talabijin na Sin wato CMG da ma’aikatar harkokin waje ta Sin da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta kasar suka shirya cikin hadin gwiwa. ’Yan siyasa da tsofaffin ’yan siyasa da shugabannin kafofin watsa labarai da sauran wakilai fiye da 50 daga kasashe ko yankuna fiye da 40 sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo, inda suka taya murnar shirya bikin.
Bana ne ake cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar gina “Ziri daya da hanya daya”. Jigon bikin fina-finai na Sin na wannan karo shi ne “Ziri daya da hanya daya”. Kafar CGTN wadda ke karkashin CMG ce ta tsara wadannan fina-finai fiye da 60 cikin harsunan Turanci da Sifaniyanci da Faransanci da Larabci da kuma Rashanci.
Masu kallo na ketare za su iya kallon fina-finan a kafofin watsa labarai kusan 100 na duniya da kuma cibiyoyin al’adun kasar Sin dake ketare. Hakan zai sa a fahimci yadda kasashe daban daban suke neman ci gaba da kuma mu’amala da sada zumunta tsakaninsu da kasar Sin bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”. (Safiyah Ma)