An bude bikin al’adun Confucius na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2024 a birnin Qufu dake lardin Shandong na kasar a jiya Jumma’a. Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma ministan sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS Li Shulei, ya halarci bikin kuma ya sanar da bude shi.
Baki da suka halarci bikin daga sassan kasar Sin da na kasashen waje na da ra’ayin cewa, tunanin Confucius ya taka muhimmiyyar rawa wajen bunkasa wayewar kan dan Adam.
- Xi Ya Yi Kira Ga Ma’aikatan Masana’antu Da Su Ba Da Gudummawar Farfado Da Arewa Maso Gabashin Sin
- Gwamnatin Tarayya Ta Bayar da Hutu Ranar Talata Don Bikin Murnar Samun Ƴanci
Kaza lika bikin al’adu na Confucius ya zama wani dandali dake aiwatar da ajandar wayewar kan duniya, da kuma zurfafa mu’ammalar wayewar kai, kana bikin na ci gaba da ba da gudummawa wajen inganta tattaunawa game da wayewar kan kasa da kasa, da inganta zumunci tsakanin al’ummun kasashen duniya da dai sauransu.
Bikin al’adun Confucius na kasa da kasa na Sin na 2024, na da jigon “Tattaunawa tare da Confucius, da fahimtar juna a fannin wayewar kai”, wanda gwamnatin jama’ar lardin Shandong, da ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta Sin, da sauran hukumomi suka dauki nauyin gudanarwa tare. (Safiyah Ma)