A yau Talata ne aka bude bikin baje kolin samar da kayayyaki na duniya na kasar Sin mai lakabin CISCE karo na biyu a birnin Beijing wanda ya kasance bikin baje koli na farko na cikin gida da ya mayar da hankali a kan hanyoyin sarrafa kayayyaki da samar da su a sassa daban-daban.
Bikin baje kolin ya kasance wani dandali da ke bayar da cikakkiyar damar daidaita kasuwanci da nufin karfafa hadin gwiwa a tsakanin masana’antu daban-daban.
Mai taken “Sada duniya domin makoma ta bai-daya”, bikin baje kolin na bana ya mayar da hankali ne kacokan a kan sada tushen samarwa bisa tsararrun hanyoyin da aka shimfida da kuma sassan baje koli, inda hakan zai assasa cikakken baje kolin muhimman hanyoyin sarrafa kaya da samar da su a tsakanin masu samarwa daga tushe da kuma masu samarwa na kusa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)