A yau Asabar ne aka bude bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing karo na 13, a cibiyar taruka ta kasa da kasa ta tabkin Yanqihu na birnin Beijing.
A yayin bikin, shugaban babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, kuma shugaban kwamitin shirya bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing a wannan karo Shen Haixiong, ya yi jawabi tare da sanar da bude bikin.
A cikin jawabinsa, Shen ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, an samu babban ci gaban fasahohin zamani. Kana ana fuskantar kalubaloli da damarmmaki a sha’anin fina-finai. Ya ce CMG za ta ci gaba da yin bayani game da labaran Sin ta hanyar fina-finai da bidiyo, da kuma yin musayar ra’ayoyi tare da abokai na kasa da kasa game da wayewar kai.
Taken bikin a wannan karo shi ne “kallon fina-finai tare da yin musayar ra’ayoyi game da wayewar kai”. Bikin ya hallara kwararru masu aikin fina-finai na kasa da kasa, tare da nuna fina-finai masu kyau, da yin hadin gwiwa a tsakanin masana’antun fina-finai, da kuma sa kaimi ga yin mu’amala da koyi da juna a tsakanin sassan kasa da kasa. (Zainab)