A yau Asabar 25 ga watan Maris din nan ne aka kaddamar da dandalin tattauna harkokin samar da ci gaba na kasar Sin, ko CDF na shekarar 2023, a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, dandalin da ya hallara wakilai daga sassan duniya daban daban, da hukumomin kasa da kasa, da manyan masana, inda ake fatan maida hankali ga tattauna muhimman batutuwa da suka jibanci tattalin arziki.
Taken taron na yini 3 shi ne “Farfado da tattalin arziki: Damammaki da hadin gwiwa”, kuma mahalartan sa za su maida hankali, ga zakulo damammakin da kasuwannin kasar Sin ke samarwa duniya, da kiyaye daidaiton tsarin samar da hajoji daga masana’antun duniya, da batun sauya akalar ci gaba zuwa fasahohin ba sa gurbata muhalli.
Da yake tsokaci game da taron, mataimakin shugaba, kuma babban sakataren asusun bincike kan samar da ci gaba na kasar Sin Fang Jin, ya ce burin da ake da shi a dandalin na CDF na bana, shi ne cin gajiya daga musaya, tare da gabatarwa duniya irin ci gaba da Sin ta samu a tafarkin ta na zamanantar da kasa, da kuma burin ta a nan gaba. Kaza lika ana fatan dandalin zai ba da damar sauraren shawarwari daga dukkanin sassa, dangane da sauye sauye da ci gaban kasar Sin, da zakulo damammakin samar da ci gaba ta hanyar hadin gwiwa, da karfafa kwarin gwiwa, da karsashin sassan ‘yan kasuwar kasa da kasa, ta yadda za su samu bunkasuwa tare da kasar Sin. (Saminu Alhassan)