A yau Alhamis 1 ga watan Mayu ne aka bude kashi na uku na bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin wanda aka fi sani da Canton Fair karo na 137, inda kamfanoni 12,043 ke halarta, tare da mayar da hankali a kan taken bikin mai lakabin “Rayuwa Mai Kyau”.
Kashi na uku na bikin Canton Fair na bana ya kunshi sassa biyar tare da wuraren baje koli guda 21, wadanda suka hada da na kayan wasan yara da kayan jarirai, da tufafi, da kayan gida, kayan rubutu da karatu, da na kiwon lafiya da kuma na nishadi.
- Kasar Sin Ta Yi Kiran Kawar Da Makaman Nukiliya Bisa Tsarin Tsaro Na Bai Daya
- Nijeriya Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Karatun Alƙur’ani Mai Girma Ta Duniya
Bisa zurfafa bincike kan bukatun masu sayayya, kamfanoni masu baje kolin hajojinsu, sun kaddamar da karin samfuran kayayyaki na musamman masu inganci, inda ta hakan suka zo da wani sabon salo na kyautata rayuwa da ba da gudummawa ga habaka samar da rayuwa mai inganci.
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi 50 cikin dari a wajen bikin Canton Fair karo na 137.
Ana gudanar da bikin Canton Fair karo na 137 ne a matakai uku, daga ranar 15 ga Afrilu zuwa 5 ga Mayu. Kashi na farko da na biyu sun jawo hankulan masu sayayya fiye da 220,000 daga kasashe da yankuna 219 na duniya, inda suka kafa sabon tarihi a lokaci guda.
Wannan ya nuna yadda kasuwancin kasashen waje na kasar Sin ya tsaya kyam da kafafunsa tare da karin kuzari, kana ya kara wa kamfanoni kwarin gwiwar yin bincike kan yadda za su ci gajiyar kasuwanni daban daban. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp