• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Bude Rumfar Sin Kan Babban Taron Sauyin Yanayi Na MDD A Birnin Dubai

by CGTN Hausa
2 years ago
Dubai

LABARAI MASU NASABA

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

A jiya ne, aka bude rumfar kasar Sin na babban taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 (COP28). An gudanar da bikin bude taron ne a yankin Blue Zone na birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ministan muhalli na kasar Sin Huang Runqiu, da manzon musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua, suka halarci bikin.

A yayin bikin bude taron, Huang Runqiu ya bayyana cewa, kasar Sin na nacewa ga samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fitar da karancin sinadarin Carbon da samun ci gaba mai inganci, da aiwatar da dabarun raya kasa don tinkarar matsalar sauyin yanayi yadda ya kamata, da yin alkawarin kiyaye kololuwar iskar carbon, da shigar da shi cikin matakan kololuwar kiyaye yanayi, da wayewar muhalli da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa baki daya.

  • Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Dabarun Warware Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa
  • Sin Ta Kammala Tsara Aikin Tauraron Dan Adam Mai Nisa Na Farko Domin Samar Da Hidimar Intanet Mai Inganci

A shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da kasashen duniya, domin samun nasarar taron COP28, da sa kaimi ga kafa tsarin gudanar da harkokin yanayi na duniya cikin adalci, da ma’ana, da hadin kai da samun nasara, da gina duniya mai tsafta da kuma kyau tare.

Xie Zhenhua ya bayyana cewa, a matsayinta na babbar kasa mai tasowa dake sauke alhakin dake wuyanta, kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali kan aiwatar da dabarun kiyaye sauyin yanayi. Kasar Sin ta zama babbar kasar da ke samar da na’urorin samar da wutar lantarki bisa karfin iska da baturan dake samar da wutar lantarki, lamarin da ya yi matukar rage farashin makamashin da ake iya sabuntawa a duniya tare da taimakawa kasashe masu tasowa samun makamashi mai tsafta, da za su dogaro a kai kuma mai araha. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou
Daga Birnin Sin

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Next Post
Wakilin Sin Ya Yi Tir Da Matakan Matsin Lamba Da Nufin Dakile Tsarin Jagoranci Da Ci Gaban Duniya

Wakilin Sin Ya Yi Tir Da Matakan Matsin Lamba Da Nufin Dakile Tsarin Jagoranci Da Ci Gaban Duniya

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.