Kafofin watsa labaru na kasa da kasa na ganin cewa, yankin Macao ya zama abin misali wajen aiwatar da manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu, bisa sakamakon da aka samu na bunkasuwar tattalin arziki da wadata, da zaman lafiya a zamantakewar al’umma, da kuma kara mu’amala da kasa da kasa a yankin.
Abin dake tantance kyawun manufa, shi ne nasarorin da aka samu daga manufar. Yawan GDP na yankin Macao a shekarar 2023 ya karu inda ya ninka sau 7 kan na lokacin da ba ya karkashin ikon kasar Sin. Yawan GDP na kowane mutum a yankin Macao ya karu daga dalar Amurka dubu 15 a shekarar 1999 zuwa dala dubu 69 a shekarar 2023. Kana yankin Macao ya kulla dangantakar tattalin arziki da cinikayya tare da kasashe da yankuna fiye da 120, ya kuma zama memban hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 190. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya fada a gun bikin murnar cika shekaru 25 da dawowar yankin musamman na Macao kasar Sin da rantsar da sabuwar gwamnatin yankin, manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu tana da fifiko da karfi, kuma tilas ne a kiyaye manufar cikin dogon lokaci.
Ya kamata a bi manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu da samun moriya daga manufar, da tabbatar da tsaro da bunkasuwa mai inganci, da yin amfani da fifikonsa wajen kara yin mu’amala a cikin gida da kuma ketare, da yada tunani mai daraja da sa kaimi ga amincewa da bambance-bambance da zaman jituwa, wadanda su ne ka’idoji hudu da shugaba Xi Jinping ya gabatar, kuma su ne nasarorin da aka samu bayan dawo da yankin Hong Kong da yankin Macao, kana sun zama abubuwan da suka jagoranci yankunan biyu zuwa ga ci gaba da yin amfani da fifikon manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu. Manazarta sun yi nuni da cewa, wannan manufa za ta kara kawo karfi, da sa kaimi ga yankin Macao da ya shiga aikin zamanintarwa irin na kasar Sin da yin mu’amala da kasa da kasa, da kuma kasancewa babban birni na zamani mai haske a duniya. (Zainab Zhang)