Jami’ai da masana sun yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, don kara bude kofofin cin gajiyar albarkatun dabbobi da kasashen Afirka ke da su, tare da bayyana kimiyya da fasaha a matsayin muhimman ginshikan kawo sauyi a fannin.
An yi wannan kiran ne a wurin taron kimiyya da fasaha kan sarrafa albarkatun dabbobi na Afirka, wanda aka gudanar a hedkwatar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ke Addis Ababa na kasar Habasha. Ofishin jakadancin Sin a kungiyar AU da kuma ofishin kula da albarkatun dabbobi a tsakanin kasashen Afirka na AU ne suka shirya taron.
Da yake jawabi a taron, kwamishinan noma da raya karkara da tattalin arzikin muhallin ruwa da kiyaye dorewar muhalli na kungiyar AU, Moses Vilakati, ya ce sana’ar kiwo na da matukar muhimmanci ga rayuwar mazauna yankunan karkara na Afirka, kuma tana da matukar muhimanci ga samar da wadataccen abinci da abinci mai gina jiki a nahiyar, da kuma hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka da kuma tsakaninsu da kasashen duniya.
Vilakati ya yi gargadin cewa, rashin kawo sauyi a fannin sana’ar kiwon dabbobi, zai haifar da koma-baya ga bunkasar masana’antu a cikin gida, da rage guraben ayyukan yi, da rage kudin shiga ga makiyaya.
A cewarsa, taron zai samar da hadin gwiwa tsakanin kwararru da masana na kasashen Afirka da na kasar Sin da sauran cibiyoyi wajen musayar gogewa da ilmi, da ba da gudummawa ga ci gaban fannin kiwo na Afirka.
A nasa bangaren, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar AU, ya bayyana cewa, masana’antar kiwo ta kasar Sin ba wai kawai ta hau kan wani babban matsayi a fannin samar da wadatattun kayayyaki da ingantacciyar masana’anta ba ce, har ma ta nuna kuzari mai karfi wajen kirkiro da fasahohi da samar da hikimomin sarrafa kaya.
Ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a bangarori daban-daban, ciki har da inganta tsare-tsaren gwamnati, da karfafa musayar fasahohi, da tallafa wa hadin gwiwar kamfanoni da ke tafiyar da harkokin kasuwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













