Shugaban Jami’a Afe Babalola Unibersity, da ke Ado Ekiti (ABUAD), Are Afe Babalola, SAN, ya kara kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya nemi kasashen Turai su yafe wa Nijeriya basukan da suke binta.
Babalola ya kuma nemi a gudanar da bincike a kan yadda Nijeriya ta samu kanta a wannan hali na kaurin basuka da ta samum kanta a halin yanzu.
- Da Ɗumi-ɗumi: Bayan CBN, FAAN, Manyan Ma’aikatun Hukumar Man Fetur Na Shirin Komawa Legas
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan Ɗaya Don Aikin Kiwon Lafiya Kyauta Ga Marasa Ƙarfi A Jihar
Ya ce a saboda haka ya kamata a dauki matakin gaggawa don a kauce wa durkushewar kasar a fannin tattalin arzki da zamantakewa.
Shugaban na jami’ar ABUAD ya yi wannan bayanin ne a garin Ado Ekiti a yayin bikin kadamar da likitoci 161 da jami’ar ta yaye.
Ya kuma kara da cewa, Nijeriya ce kasar da tafi kowacce kasa bashi a duniya. A kan haka ya kamata a gudanar da biciken don gano yadda muka kai ga cin bashin tiriliyoyin nairori, mai muka yi da bashin? ina mai tabbatar muku da cewa, yawwancin kudaden na a aljihun wadanda suka ciwo basukan.”
Daga nan ya kuma nemi gamnatin tarayya ta dauki darasi a kan abin da tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya yi a lokacin da Nijeriya ta samu kanta a irin wannan halin, “Idan ba mu yi haka ba basuka za su durkusar da kasar mu wanda hakan na iya haifar da komai.
“Naga mutane musamman daga arewacin Nijeriya, suna kuka saboda al’amurra na ci gaba da tabarbarewa, darajar naira na kara karyewa, farashin kayan abinci yana ta hauhawa, babu aikin yi, wadanda ke aikim kuma babu albashi. Dalilin haka kuma shi ne babu kudade, kuma darajar naira na kara karyewa. Dole a dauki matakin da ya dace don ceto kasar nan.” In ji shi.