Rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa ta cafke wani mai suna Abubakar Mohammed dan shekara 23 wanda daya ne daga cikin fursunonin da suka arce daga gidan gyara hali na Kuje dake Abuja.Â
Abubakar wanda ake tuhuma da aikata ta’addanci, yana tsare ne a gidan gyara halin na Kuje tun shekarar 2017 kafin ‘yan ta’addan Boko Haram sukai hari gidan gyara halin.
A cikin sanarwar da Kwamishinan Rundunar, CP Sikiru Akande ya rattaba wa hannu, ya ce, Abubakar ya shaida wa Rundunar cewa, tun 2017 yake tsare a gidan yarin bayan ya samunsa da hanu a aikata ta’addanci.
An cafke Abubakar ne a jiya Laraba a kan hanyar sa ta shiga jihar Borno wacce itace asaljn jiharsa.
Sikiru ya kara da cewa Rundunar ta kuma kama wasu mutum 12 da take zargi da aikata manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami da sauran su.