Jami’an Hukumar Yaki Da Safarar Mutane (NAPTIP) sun ceto akalla yara 26 da aka yi safarar su daga wani gidan marayu a Jihar Binuwe, tare da kama wasu ma’aikatan gidan marayu guda hudu bisa zargin sayar da yaran da aka safara yi tsakanin Naira miliyan 1 zuwa miliyan 3.
Mai magana da yawun NAPTIP na kasa, Bincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
A cewar Adekoye, cikin wadanda aka kama akwai wani mai shekaru 60 da ke cikin kungiyar masu mallakar gidajen marayu a Nijeriya, sannan shi ne wanda ya kafa wata kungiyar kare hakkin yara ta duniya, mai suna National Council of Child’s Rights Adbocates of Nigeria.
- Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
- Davido Ya Yi Alƙawarin Tallafin Miliyan 300 Ga Marayu
Ya bayyana cewa wadannan mutane ana zarginsn safara da kuma sayar da fiye da yara 300 suna boye gaskiya da sunan karbar daukar nauyin marayu (adoption), inda daga cikinsu ne aka ceto yara 26.
Sanarwar ta ce, “A wani gagarumin sumame da jami’an hukumar, sashen Makurdi, suka jagoranta, hukumar ta ceto yara 26 daga cikin fiye da yara 300 da ake zargin an yi safarar su tare da sayar da su ga mutane daban-daban a cikin jihohin Binuwe, Enugu, Legas, Nasarawa da kuma Abuja, yayin da ake ci gaba da bin diddigin sauran yara kusan 274, domin gano cikakken yadda wannan kungiya ke gudanar da miyagun ayyukanta.
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.”
Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.”
Ya kara da cewa, daya daga cikin masu korafin ya bayyana cewa ya biya Naira miliyan 2.8 a matsayin kudin daukar yaro, sannan ya biya Naira 100,000 a matsayin kudin shawara ga daya daga cikin ‘yan kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wani mai korafi ya ce shi ma ya biya Naira miliyan 2.8 kudin daukar yaro da Naira 100,000 kudin shawara ga wani dan kungiyar.
“An canza sunayen yawancin yaran da aka ceto, lamarin da ya kara wahalar da bincike da gano asalinsu,” in ji sanarwar.
Darakta Janar ta NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta bayyana damuwarta kan wannan lamari, inda ta ce safarar yara ta zama babbar matsala a kasa.
Ta hanyar Adekoye, DG din ta nuna damuwa game da yadda wasu gidajen marayu ke amfani da raunin jama’a wajen aiwatar da safarar yara.
Ta ce, “Abin takaici ne yadda wasu masu mugunta da ke da sunayen kwararru da matsayi a cikin al’umma, suke amfani da matsayin su wajen yaudarar mutanen da ke cikin mawuyacin hali, su yi safarar ‘ya’yansu, da dama daga cikinsu ma sun tsira ne daga halaka a lokacin rikice-rikicen al’umma ko na manoma da makiyaya, sannan a sayar da su ga iyaye masu neman haihuwa a matsayin daukar yaro ba tare da sahihin izinin iyayensu ba.
“Wannan abin ba za a yarda da shi ba, kuma wadanda aka kama kan wannan mugun aiki za su fuskanci hukuncin doka yadda ya kamata.
“’Ya’yanmu ba kayayyaki ba ne da za a ajiye su a gidajen marayu a sayar ga mai biyan mafi tsada. Wannan dole ya tsaya,” in ji ta.














