Jami’an tsaro sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin sun ba da bayanan sirri ga ‘yan bindigar da suka kai hari gidan yarin Kuje, da ke Abuja.
An rawaito cewar wata majiya mai karfi ta hukumar leken asiri ta kasa ta tabbatar da kamen.
- Wadanda Suka Sace Jaruman Nollywood Sun Bukaci Dala Dubu 100,000 A Matsayin Kudin Fansa
- Kasar Sin Ta Bukaci A Gina Daidaitaccen Tsarin Tsaro Na Duniya Da Na Shiyya-shiyya
An cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsofaffin wayoyin hannu da basa amfani da Intanet.
Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen ta ce ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.
Maharan da ake zargi da kai hari a wasu sassan yankunan Abuja, a cewar majiyar.
Yanzu haka ana tsare da mutanen da aka cafke kuma ana ci gaba da tuhumarsu domin amsa tambayoyi.
Hakazalika, an rawaito cewa hukumar tsaro ta Najeriya na tattara bayanan sirri domin gano masu hannu a matsalolin tsaro da hare-haren da ake kitsawa.
Idan za a iya tunawa a farkon watan Yuli ne, wasu mahara suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda suka kashe jami’an tsaro sannan suka tseratar da fursunoni da dama.