Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce an kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan mutanen Kaduna 12 a Jihar Filato.
Waɗanda aka kashe suna kan hanyar tafiya ne daga Zariya a Jihar Kaduna zuwa bikin aure da za a yi a ƙaramar hukumar Quan Pan da ke Jihar Filato.
Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya
Amma sun faɗa hannun wasu matasa a unguwar Mangun da ke ƙaramar hukumar Mangu, inda suka kashe su.
Wasu kuma sun jikkata a harin.
Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika.
Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina.
Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari.
Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp