Majalisar dattawa ta amince da tsawaita wa’adin watanni shida ga kasafin kudin kasar na shekarar 2024, daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 31 ga Disamba, 2025.
An yanke shawarar ne yayin zaman majalisar a ranar Talata, biyo bayan gabatarwa da kuma saurin amincewa da kudirin yin kwaskwarima ga dokar kasafin ta shekarar 2024.
- Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Dukkan Fasinjojin Motar Bas A Jihar Benuwe
Kudirin gyaran dokar da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi, Sanata Solomon Adeola (APC, Ogun ta Yamma) ya dauki nauyin yi, an yi karatu na daya da na biyu da na uku a lokaci guda.
Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki.
Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga.














